Abba Kabir Ya Yi Martani Mai Zafi ga Kwankwaso, Ya Tabo Batun Girman Ganduje a Kano

Abba Kabir Ya Yi Martani Mai Zafi ga Kwankwaso, Ya Tabo Batun Girman Ganduje a Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana kansa a matsayin jagoran APC a Kano bayan komawa jam'iyyar daga NNPP
  • Abba Kabir ya bayyana cewa bai karkashin tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje duk da sauya sheƙarsa daga NNPP
  • Gwamnan ya mayar da martani ga Rabiu Kwankwaso, inda ya ce sauya sheƙarsa ya biyo bayan rikicin cikin gida na NNPP, ya musanta zargin cin amanar Kwankwasiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana game da tasirinsa cikin jam'iyyar APC bayan dawo wa cikinta.

Gwamnan ya bayyana kansa a matsayin jagoran APC a Kano, yana mai cewa ba ya karkashin Abdullahi Ganduje a harkokin siyasa.

Abba Kabir ya yi martani ga Kwankwaso game da siyasar Kano
Gwamna Abba Kabir, tsohon gwamna Abdullahi Ganduje da Sanata Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Abba Kabir ya yi wannan bayani ne yayin mayar da martani kan suka da suka biyo bayan sauya sheƙarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a jihar, cewar Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

"Idonmu na kan ku": Kwankwaso ya tura sako bayan zanga zangar adawa da matakin INEC

Martanin Abba Kabir ga Sanata Rabi'u Kwankwaso

Jagoran siyasar Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso ya soki matakin, yana zargin Abba Kabir da cin amanar tafiyar Kwankwasiyya ta hanyar mika nasarar da aka samu ga Ganduje.

Da yake magana da magoya baya da manema labarai, gwamnan ya ce rikicin cikin gida na NNPP ne ya tilasta masa sauya sheƙa domin kaucewa matsaloli.

Ya ce:

“Ina tabbatar da cewa ba mu aikata wani laifi ba wajen ficewa daga tafiyar da muka kasance a ciki, mun yi gargadi amma ba a saurare mu ba.”

Abba ya kara da cewa sun dauki mataki da wuri domin hana rikicin shafar miliyoyin jama’a a Kano, yana mai cewa yanzu zaman lafiya ya samu.

Gwamnan ya musanta zargin cin amanar Kwankwasiyya, yana cewa su ma ba a tuntubi mambobin tafiyar ba kafin wasu su sauya sheƙa zuwa ADC.

Ya kara da cewa:

“Yanzu ana zargin mu da cin amana, amma su da suka fice daga NNPP ba tare da tuntuba ba, wannan ba cin amana ba ne?”

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya magantu kan takarar 2027 da zama mataimakin Obi a ADC

Abba Kabir ya bayyana jagoran jam'iyyar APC a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano yayin taro a gidan gwamnati. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Abba Kabir ya fadi jagoran siyasar Kano

Gwamna Abba ya kuma tambayi wanda ke rike da ragamar APC a Kano, inda magoya bayansa suka amsa da cewa shi ne jagoran jam’iyyar a yanzu, kamar yadda Premier Radio ta wallafa a Facebook.

Ya ce shiga APC ya sanya shi cikin gwamnonin fiye da 31, yana tambayar ko hakan koma baya ne ko kuma babban ci gaba ga siyasar Kano.

A karshe, Abba ya jaddada cewa yana girmama Ganduje, amma ba zai amince a rika ba shi umarni ba, domin shi ne jagoran APC a Kano.

An shawarci Abba Kabir kan nadin mataimaki

Mun ba ku labarin cewa jigon APC a Kano, Garba Kore Dawakin Kudu, ya shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zaɓi mataimaki mai jama’a domin nasarar 2027.

Ya ce su aiki za su yi tsakani da Allah domin Abba ya koma kujerar gwamna, Abba sai ya dauki mai jama'a a dukkanin kananan hukumomi.

Jigon ya bayyana haka ne a lokacin da aka cewa gwamnatin tarayya da majalisar dokokin Kano ke da zabinsu a kujerar, kuma an ci karo a wanda ake so.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.