Abba Ya Fara Jefo Maganganu tun bayan Barinsa NNPP zuwa APC a Kano

Abba Ya Fara Jefo Maganganu tun bayan Barinsa NNPP zuwa APC a Kano

  • Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya zargi tsohon mataimakinsa da yunkurin kwace masa kujerar ta hanyar shirya markashiya
  • Ya bayyana haka ne a maganar da ya yi karon farko tun bayan da ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC a watan Janairu na shekarar 2026
  • Da ya ke karin bayani game da murabus da mataimakinsa ya yi, ya bayyana cewa har yanzu takardar Aminu Abdussalam Gwarzo ba ta zo hannunsa ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano –Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa tsohon mataimakinsa, Aminu Abdussalam, ya yi yunkurin cire shi daga kan mulki domin ya karbi kujerarsa.

Gwamnan ya yi wannan zargi ne a ranar Alhamis 9 ga watan Afrilu 2026 yayin da ya karbi bakuncin wasu mawaka da ake kira Mawallafan Abba Gida Gida a gidan gwamnati da ke Kano.

Kara karanta wannan

Boko Haram: Tinubu ya fadi abin da zai biyo bayan kisan janar a Borno

Abba Kabir Yusuf ya ce Aminu Abdussalam ya nemi kujerarsa
Aminu AbdusSalam Gwarzo tare da gwamna Abba Kabir Yusuf suna kus-kus a wani taro a baya Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A wani bidiyo da Isah Muhammad Salisu ya wallafa a shafinsa na Facebook, gwamnan ya bayyana cewa duk da kokarin da Gwarzo ya yi, sai shi ne ya bar wurin.

Abba ya magantu kan tsohon mataimakinsa

Daily Trust ta ruwaito Gwamnan ya kara da cewa dalilin da ya sa tsohon mataimakin ya dauki wannan mataki shi ne yunkurin karbe masa kujerar gwamna, amma bai samu nasara ba.

A cewarsa, har yanzu bai ga takardar murabus din tsohon mataimakin gwamnan ba, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ba ta taba cutar da shi ba.

Ya bayyana cewa:

“Yau mataimakin gwamnan da muka zo tare a tikiti guda ba ya tare da mu. Babu wanda ya cuce shi. Har yanzu ma ban ga takardar murabus dinsa ba, me ya dame ni da ita?”
“Duk abin da ya sa ya yi haka, yunkuri ne na cire ni ya karbi mukamin, amma Allah bai yarda ba."

Kara karanta wannan

Amsar da Malam Shekarau ya ba shugaban APC bayan ya nemi ya koma jam'iyya mulki

Abba ya kare sauya shekarsa

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma mayar da martani ga masu sukar matakin da ya dauka na sauya sheka daga jam’iyyar NNPP.

Ya jaddada cewa matakin da ya dauka ba cin amana ba ne, illa kokarin kare muradun al’ummar Kano, ya ce wadanda ke zarginsa da cin amana su ma sun taba daukar irin wannan mataki a baya, amma ana yin biris da hakan.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da martani ga Kwankwaso
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf a lokacin suna 'dasawa Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Gwamnan ya bayyana cewa sun lura da alkiblar da jam’iyyar ke dauka, sun ba da shawara amma aka yi watsi da ita, wanda hakan ya tilasta masu daukar matakin ficewa domin kauce wa jefa al’ummar Kano cikin rudani.

Ya kara da cewa abubuwan da ke faruwa yanzu sun tabbatar da hujjojin da ya gabatar tun farko kafin barin jam’iyyar.

Abba ya yi martani ga Kwankwaso

A baya, mun wallafa cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana kansa a matsayin jagoran APC a Kano bayan komawa jam'iyyar daga NNPP saboda haka yanzu gashin kansa ya ke ci.

Kara karanta wannan

"Idonmu na kan ku": Kwankwaso ya tura sako bayan zanga zangar adawa da matakin INEC

Abba Kabir ya bayyana cewa ba ya karkashin tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje duk da sauya sheƙarsa daga NNPP, amma akwai kyakkyawar alaka ta girmamawa a tsakaninsu.

Gwamnan ya mayar da martani ga Rabiu Kwankwaso, inda ya ce sauya sheƙarsa ya biyo bayan rikicin cikin gida na NNPP, ya musanta zargin cin amanar Kwankwasiyya kamar yadda ke gani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng