DSS Ta Gano Tsohon 'Dan Majalisa da Ya Kada Hantar Amurka da Rashin Tsaro a Najeriya
- Jami’an tsaro sun kama tsohon ɗan majalisar tarayya, Aliyu Gebi, bisa zargin bayar da rahoton tsaro na ƙarya ga ofisoshin jakadanci
- Rahoton da ake zargin ya haddasa tashin hankali har wasu kamfanonin jiragen sama suka soke zirga-zirga zuwa Najeriya saboda rahoton
- Ana ci gaba da bincike duk da cewa an bayar da belinsa, ana kuma shirin gurfanar da shi a kotu domin bibiyar batun kamar yadda doka ta tana
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Rahotanni sun bayyana cewa jami’an hukumar tsaron farin kaya (SSS) sun kama Aliyu Gebi, wani ɗan siyasa kuma mai ba da shawara kan tsaro, a ranar Juma’a 3 ga watan Afrilu, 2026.
Majiyoyi masu tushe sun ce an kama shi ne bisa zargin ya bayar da bayanan sirri na tsaro da ba su da inganci ga wasu ofisoshin jakadancin ƙasashen waje da ke Najeriya.

Kara karanta wannan
Wahalar da na sha a APC ko shugaban jam'iyya bai sha ba in ji Diyar Buba Galadima

Source: Twitter
A labarin da ya kebanta ga jaridar Premium Times Gebi, wanda ya taɓa zama ɗan majalisar wakilai a majalisa ta bakwai, ya zama fitaccen mutum a fannin tsaro a Najeriya.
DSS na zargin tsohon 'dan majalisa da karya
Rahoton ya ce ana zargin Gebi aikawa jakadanci rahoton da jami’an tsaro suka bayyana a matsayin “ƙarya”, wanda ya janyo ruɗani da tashin hankali a tsakanin ƙasashen waje.
Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya ce wannan rahoto ya sa wasu kamfanonin jiragen sama daukar matakai marasa dadi.
Ya ce kamfanin jiragen sama na Lufthansa ya soke wasu jirage da suka shirya zuwa Najeriya, yayin da British Airways ma ta kusa daukan irin wannan mataki.
Har ila yau, wata majiya ta ce Amurka ta dogara da irin wannan rahoto wajen fitar da gargadin tsaro ga ‘yan kasarta da ke Najeriya.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bukaci ma’aikatan da ba su da muhimmanci su fice daga kasar, tana mai nuni da tabarbarewar tsaro.
DSS na binciken tsohon 'dan majalisa
Gwamnatin Najeriya ta musanta wannan ikirari na cewa akwai gagarumar barazanar tsaro a kasa, tana mai cewa ana samun ci gaba wajen inganta tsaro.
A cikin sabon gargadin tafiya, Amurka ta bayyana cewa laifuffuka kamar fashi da makami, garkuwa da mutane da hare-haren ‘yan bindiga suna yawaita a wasu sassan Najeriya.
Ko da yake ba a samu cikakken bayanin abin da rahoton Gebi ya ƙunsa ba, majiyoyi da dama sun ce ya haifar da matsaloli a harkokin diflomasiyya.
Wasu jakadanci sun yi shirin daukar mataki bisa rahoton, amma bayan tattaunawa da gwamnatin Najeriya sai suka dakatar da shirin.
A halin yanzu, an bayar da belin Gebi, amma ana ci gaba da bincike a kansa. Rahotanni sun nuna cewa yana ci gaba da zuwa hedikwatar DSS domin amsa tambayoyi.
Ana sa ran za a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike, sai har yanzu bai ce komai a kan zargin da ake yi masa ba.
Amurka ta dauki mataki a Najeriya
A baya, mun wallafa cewa Amurka ta soke duka bukatun da 'yan Najeriya suka shigar domin neman bizar zuwa kasar a babban birnin tarayya Abuja ba tare da ta sanar da lokacin ci gaba da aikin ba.
Wannan mataki na zuwa ne awanni bayan Amurka ta umarci duka jami'anta da ayyukansu ba su zama wajibi ba su shirya barin Najeriya saboda tsanantar rashin tsaro da ake samu a sassan kasar.
Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya gargadi Amurkawa da su gujewa zuwa jihohi 23 da aka sanya a rukunin gargadi na hudu, inda ta bayyana cewa akwai babbar barazanar tsaro a jihohin.
Asali: Legit.ng

