Ci Gaba Ko Baya? Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC Ya Samu Mukamin Kwamishina

Ci Gaba Ko Baya? Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC Ya Samu Mukamin Kwamishina

  • Majalisar dokokin Kogi ta amince da tsohon shugaban APC na jihar a matsayin kwamishina bayan bukatar Gwamna Ahmed Usman Ododo
  • ‘Yan majalisar sun yabawa tsohon shugaban APC bisa rawar da ya taka wajen nasarorin zabe na jam’iyya
  • Sabon kwamishinan ya ce APC ba ta da hamayya mai karfi a Kogi, yana mai jaddada cewa zaben 2027 zai zama mai sauki ga jam’iyyar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lokoja, Kogi - Majalisar dokokin Kogi ta tantance tare da amincewa da tsohon shugaban jam’iyyar APC a matsayin kwamishina.

Tsohon shugaban APC na jihar, Abdullahi Bello, ya zama kwamishina ne bayan tura sunansa majalisar da Gwamna Usman Ododo ya yi.

Tsohon shugaban APC ya zama kwamishina a Kogi
Gwamna Usman Ododo na Kogi da sabon kwamishina, Abdullahi Bello. Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo, Ramat Molo Aliyu.
Source: Facebook

Tsohon shugaban APC ya zama kwamishina

Yayin zaman majalisa, an duba cancantar Bello tare da amincewa da nadin nasa bayan tantance shi bisa tanadin kundin tsarin mulki, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Kujerar mataimakin Abba Kabir na neman jawo rigima, an roki Tinubu kan Sule Garo

Bayan tantancewar, an tabbatar da shi a matsayin kwamishina, inda ake yi masa lakabi da “Dollar” a tsakanin magoya bayansa.

‘Yan majalisa sun yabawa tsohon shugaban APC din kan rawar da ya taka wajen tabbatar da nasarorin zabe na jam’iyyar a jihar.

Sun bayyana cewa gogewarsa da kwarewarsa za su taimaka wajen karfafa harkokin mulki da inganta ayyukan gwamnati ga al’ummar Kogi.

Gwamna ya ba tsohon shugaban APC mukamin kwamishina
Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi a taron majalisar zartarwa a Lokoja. Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo.
Source: Facebook

Martanin sabon kwamishina a Kogi

Da yake magana bayan amincewa da shi, Bello ya yi alkawarin kawo karin ci gaba musamman ga ma’aikatan kananan hukumomi a fadin jihar.

Ya gode wa Gwamna Ododo bisa ba shi wannan dama, yana mai cewa zai yi aiki bisa tsarin da aka kafa domin inganta harkokin mulki, cewar Premium Times.

Bello ya jaddada cewa abin da zai fi bai wa fifiko shi ne walwalar ma’aikatan kananan hukumomi da inganta ayyukansu.

Ya ce:

“Duk abin da zai inganta jin dadin ma’aikatan kananan hukumomi shi ne zan bi, kuma hakan ne babban abin da na sa a gaba.
“Kogi na daukar darasi daga Shugaba Tinubu, babban bawan Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo, na aiki tukuru domin cika bukatu da burin al’umma ta hanyar bin sawun shugaban kasa.”

Kara karanta wannan

APC ta fadi abin da zai hana 'yan adawa kwace mulkin Najeriya

Game da zaben 2027, ya bayyana cewa babu wata jam’iyyar adawa mai karfi da za ta iya kalubalantar jam'iyyar APC a Kogi.

Ya danganta karfin jam’iyyar da nasarorin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa shugaban ya samu goyon bayan ‘yan Najeriya.

A karshe, Bello ya ce zaben 2027 zai kasance mai sauki ga APC a jihar, yana mai hasashen cewa jam’iyyar za ta lashe dukkan kujeru ba tare da wata matsala ba.

Tsoho shugaban APC a Kogi ya rasu

A baya, mun ba ku labarin cewa an shiga jimami da rudani a jihar Kogi bayan rasuwar shugaban jam'iyyar APC na shiyyar Kogi ta Gabas.

Suleiman Omika Mohammed ya rasu ne lokacin da yake cikin hutawa a gidansa da ke birnin Lokoja, babban birnin jihar.

Mataimakin gwamnan Kogi, Joel Salifu ya yi ta'aziyya kan wannan babban rashin da APC ta yi na ɗaya daga cikin shugabanninta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.