Kotu ta soke zaben dan majalisar APC a Kogi

Kotu ta soke zaben dan majalisar APC a Kogi

- Kotu ta soke takarar dan majalisar dokokin jihar Kogi, Atule Egbunu, mai wakiltar mazabar Ibaji a jihar

- Kotun ta yanke wannan hukuncin ne sakamakon karar da Joseph Enemona ya shigar da kallubalantar zaben fidda gwani da APC ta yi

- Alkalin ya jadada cewa APC bata bi doka ba wurin yin zaben fidda gwani ya kuma bada umurnin a maye gurbin dan majalisar da dan takarar jam'iyyar PDP da ya zo na biyu a zaben

Wata kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Abuja ta soke zaben dan majalisar jihar Kogi, Atule Egbunu, mai wakiltar mazabar Ibaji da ya aka zaba a karkashin jam'iyyar APC, The Nation ta ruwaito.

A madadinsa, Mai shari'a Inyang Ekwo ya bada umurnin a maye gurbinsa da dan takarar jam'iyyar ta ya zo na biyu a zaben rabar gardama na 5 ga watan Disambar 2020 wadda Egbunu ya yi nasara.

KU KARANTA: Shekau ya fitar da sabon sautin murya, ya gargadi sabbin shugabanin sojoji da Buhari ya naɗa

Kotu ta soke zaben dan majalisar APC a Kogi
Kotu ta soke zaben dan majalisar APC a Kogi. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

Mai shari'a Ekwo ya bada wannan umurnin ne a ranar Juma'a da ya ke yanke hukunci a kan karar da aka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/173/2020 da Joseph Enemoma ya shigar inda ya kallubalanci zaben fidda gwani da jam'iyyarsa ta APC ta yi domin zaben dan takarar da zai fafata a zaben raba gardamar.

DUBA WANNAN: Wadanda Buhari ya naɗa manyan hafsoshin sojoji sun cancanta, in ji Shettima

INEC ta sanar da cewa Egbunu na APC ne ya lashe zaben da kuri'u 8,515 yayin da dan takarar PDP, Daniel Enefola ya zo na biyu da kuri'u 4,564.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags:
APC