Rigima Ta Kunno Kai a APC bayan Gwamna Ya Nuna Sha'awar Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar
- Yunkurin Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed na sauya sheka daga PDP zuwa APC ya raba kan jiga-jigan jam'iyyar
- Kungiyar yan Majalisar tarayya na APC daga Bauchi ta yi watsi da shirin sauya shekar Gwamna Bala, sun kafa hujja da sukar Bola Tinubu
- Sai dai wasu kusoshin APC a Bauchi sun saba wa wannan ra'ayi, inda suka bayyana cewa a shirye suke su karbi Gwamna Bala
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi, Nigera - An fara samun rabuwar kai tsakanin masu ruwa da tsakin APC na jihar Bauchi saboda yunkurin Gwamna Bala Mohammed na komawa jam'iyya mai mulkin kasa.
Magoya bayan Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, sun kara kaimi wajen ganin ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, duk da adawar da wasu jiga-jigan jam’iyyar a jihar suka nuna.

Source: Twitter
'Yan Majalisar APC na Bauchi sun toshe kofa
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa kungiyar 'yan Majalisar tarayya na APC a Bauchi ta bayyana kin amincewarta karara da shirin karbar gwamnan.
A wani taro da suka gudanar a Abuja, mambobin kungiyar sun ce shigar gwamnan Bauchi a wannan lokaci zai iya kwo rabuwar kai a jam’iyya, rage amincewar jama’a ga APC da kuma lalata damar nasara a zaben 2027.
Shugaban yan majalisar kuma Sanatan Bauchi ta Arewa, Sama’ila Kaila Dahuwa, ya bayyana cewa sun yi watsi da yunkurin shigar gwamnan APC kai tsaye.
Dalilan kin amincewa da Gwamna Bala
Ya ce gwamnan ya dade yana sukar Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da kuma manufofin jam’iyyar APC, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
A cewarsa har yanzu Gwamna Bala bai janye kalamansa ba, bai nemi sulhu da shugabannin jam’iyyar ba kuma bai nemi gafara a bainar jama’a ba
Saboda haka, ya ce ba za su goyi bayan duk wani mataki da zai kawo cikas ga zaman lafiyar jam’iyyar APC a jihar Bauchi ba.
An fara samun sabani cikin jam'iyyar APC
Sai dai duk da wannan matsaya, wasu jiga-jigan APC a jihar Bauchi sun nuna goyon bayansu ga shirin sauya shekar Gwamna Bala Mohammed.
Wani babban jigo a jam’iyyar, Kwamared Aliyu Abdullahi Ilelah, ya ce yawancin mambobin APC a Bauchi a shirye suke su karbi gwamnan hannu biyu-biyu.
Ya zargi masu adawa da sauya shekar gwamnan Bauchi zuwa APC da nuna son zuciya karara domin cika burikansu na siyasa.

Source: Twitter
Ilelah ya kara da cewa abin da jagororin APC na Bauchi sauka yi rashin girmamawa ne ga shugabancin jam’iyya na kasa da kuma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
A cewarsa: Shugaban kasa da shugabannin APC na kasa na kokarin jawo gwamna Bala Mohammed amma wasu a jihar suna kokarin hana shi shiga jam’iyyar.
Gwamna Bala ya gama shirin tafiya APC
An ji cewa Gwamna Bala Mohammed ya kammala shirin barin PDP zuwa APC a wannan makon bayan tattaunawa da Shugaba Bola Tinubu.
Gwamnan Bauchi kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP, ya gana da Shugaba Bola Tinubu da shugabannin APC inda ya bayyana aniyarsa ta shiga jam'iyya mai mulki a ƙasa.
Majiyoyi sun bayyana cewa shirin sauya shekarar Gwamna Bala na iya samun alaƙa da matsin lambar da kwamishinan kuɗin Bauchi, Yakubu Adamu, ke fuskanta,
Asali: Legit.ng


