Bayan Barazanar APC, An Kafa Kwamiti game da Sauya Shekar Gwamnan Bauchi
- ‘Yan majalisar koli na APC reshen jihar Bauchi sun kafa kwamitin kan yiwuwar sauya sheƙar gwamna Bala Muhammad zuwa cikinta
- Matakin na zuwa bayan jam'iyyar ta sanar da cewa ba za ta amince da Gwamna Bala Muhammad ya dawo cikinta ba duk da rade-radin zai sauya sheka
- Amma rahotanni sun bayyana cewa taron kafa kwamitin bai yi armashi ba, domin an samu sabani sosai da musayar yawu kan batun
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi – ‘Yan majalisar dokoki na jam’iyyar APC na jihar Bauchi da ke majalisun tarayya a sun yanke shawarar kafa wani kwamitin koli domin duba shirin da gwamna Bala Mohammed, ke yi na sauya sheƙa zuwa jam’iyyar mai mulki.
Hakan ya biyo bayan sabani mai ƙarfi da ya ɓarke a tsakanin 'yan ƙungiyar a wani taro da suka gudanar a Abuja, inda aka samu ra’ayoyi mabambanta kan tasirin siyasa da tsarin jam’iyya da irin wannan sauyi zai haifar.

Source: Facebook
Nigerian Tribune ta wallafa cewa mukaddashin sakataren ƙungiyar, Dabo Ismail, ya bayyana cewa an dorawa kwamitin alhakin tsara da gabatar da bukatu da sharuddan da ƙungiyar ke da su ga shugabancin APC kan batun.
APC ta tattauna game da lamarin Gwamnan Bauchi
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Dabo Isma'il ya ƙara da cewa kwamitin zai tattauna da manyan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa an gudanar da shawarwari cikin lumana da haɗin kai.
Haka kuma zai wakilci ƙungiyar a duk wata tattaunawa da ta shafi yiwuwar sauya sheƙar gwamnan daga PDP zuwa APC, tare da rika mika ahoto akai-akai kan ci gaban tattaunawar.
Sai dai Dabo Ismail ya jaddada cewa ƙungiyar na maraba da gwamnan idan ya yanke shawarar shiga APC, amma ya buƙaci shugabancin jam’iyyar na ƙasa da ya haɗa da duk masu ruwa da tsaki na jihar wajen tattaunawar.
An kafa kwamiti a kan Gwamnan Bauchi

Kara karanta wannan
Rigima ta kunno kai a APC bayan gwamna ya nuna sha'awar sauya jam'iyya a Najeriya
Dabo Ismail ya bayyana matakin kafa kwamitin a matsayin wata hanya ta dimokuraɗiyya da za ta ba da damar sauraron ra’ayoyi daban-daban tare da kiyaye haɗin kan jam’iyya.

Source: Facebook
A nasa ɓangaren, Shugaban ƙungiyar kuma Sanatan Bauchi ta Arewa, Sama’ila Dahuwa, ya nuna rashin jin daɗinsa kan abin da ya kira rashin tuntuba daga shugabancin APC na ƙasa a kan batun.
Ya bayyana wannan lamari a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, yana mai gargadin cewa bai kamata a riƙa ɗaukar matakai ba tare da shawarwari da manyan masu ruwa da tsaki a matakin jiha ba.
Sanatan ya bayyana cewa kwamitin da aka kafa ya haɗa da manyan jam’iyyar, daga ciki har da minista mai ci, tsofaffin gwamnoni da kuma sanatoci biyu.
Haka kuma, ƙungiyar ta yanke shawarar miƙa koke-kokenta ga shugabancin APC na ƙasa, tare da jaddada buƙatar bin ƙa’idoji da kuma tuntubar juna kafin ɗaukar duk wani mataki.
Gwamnan Bauchi ya magantu kan sauya sheka
A baya, mun wallafa cewa Gwamna Bala Mohammed ya magantu kan rade-radin komawa APC, yana cewa zai ci gaba da zama a PDP duk da matsalolin da ke cikinta da fice wa da ake yi zuwa jam'iyya mai mulki.
Ya ce siyasa na iya sauyawa, amma za su dauki matakai cikin hikima da dabara ba tare da yin kuskure ba duk da rade-radin da ke yawo cewa ya kammala shirin rabuwa da jam'iyya mai adawa.
Gwamnan ya yi alkawarin biyan albashi kan lokaci da kuma warware basussukan giratuti kafin ya kammala wa’adin mulkinsa Read more:
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

