Amsar da Malam Shekarau Ya ba Shugaban APC bayan Ya Nemi Ya Koma Jam'iyya Mai Mulki
- Malam Ibarahim Shekarau ya bayyana cewa nan ba da jimawa zai yanke shawara kan yiwuwar sauya sheka daga PDP zuwa APC
- Tsohon gwamnan na jihar Kano ya fadi haka ne yayin da ya karbi bakuncin tawagar APC karkashin jagorancin shugaban jam'iyya, Nentawe Yilwatda
- Shekarau ya jinjina wa tawagar APC bisa kawo masa ziyara har gida, yana mai cewa nan da kwanaki biyu zai yanke makomarsa ta siyasa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya nuna alamun cewa yana iya ficewa daga jam’iyyar PDP, inda ya bayyana cewa har yanzu yana nazari kan wannan matakin.
Malam Shekarau ya bayyana hakan ne yayin da shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai masa ziyara gidansa da ke Kano.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ziyarar na daya daga cikin kokarin da jam’iyya mai mulki ke yi na karfafa tasirinta a yankin Arewa.
Sanata Hayatu Gwarzo ya halarci taron, inda shugaban na APC ya karfafa masa gwiwa shi ma ya dawo cikin jam’iyya mai mulki.
Shugaban APC ya mika bukatarsa ga Shekarau
Yayin tattaunawar, Yilwatda ya jaddada muhimmancin hadin kai a tsakanin shugabannin siyasa na Arewa, inda ya bayyana yankin a matsayin cibiyar siyasar Najeriya.
Ya yaba wa Shekarau a matsayin mutum mai kima wanda gogewarsa da jagorancinsa ke da daraja sosai, inda ya bukaci ya dawo jam'iyyar APC.
“Mun zo nan ne domin tabbatar da cewa Kano ta daidaita, muna rokon ka, kasancewar ka daya daga cikin ginshikan siyasar Najeriya, mai mabiya a fadin kasar nan, APC tana bukatar ka.
“Jam'iyyar APC da Shugaban kasa suna bukatar shugabanni irin ku (Shekarau) domin su taimaka, su mara baya, kuma su gina jam'iyyar don lashe zabukan shekara mai zuwa.
“Mu hadu gaba daya a APC, ba zan iya ni kadai ba, sai mun hadu ne za mu iya gina dandamali mai karfi da kwarjini domin taimaka wa Arewa."
- Nentawe Yilwatda.
Abin da Shekarau ya fada wa tawagar APC
Da yake nasa jawabin, Malam Shekarau, ya yi godiya kan wannan ziyara tare da kokawa kan kalubalen cikin gida da ke addabar PDP, kamar yadda The Guardian ta rahoto.
Shekarau ya jinjina wa Shugaban APC na kasa bisa ware lokaci don ziyartar sa, inda ya bayyana matakin a matsayin nuna girmamawa, da gaske, da kuma sadaukarwa.
“Kun zo gare mu; da kuna iya turo wani ko ma mu hadu a Abuja, amma kun zo da kanku,” in ji Shekarau.
Shekarau ya kara da cewa ziyarar ta zo a daidai lokacin da yake nazari kan makomarsa ta siyasa tare da abokan tafiyarsa.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan ya kara da cewa:
“Nan da kwana biyu ko nan da ‘yan kwanaki kadan, zan sanar da matsaya ta. Kun zo ne a lokacin da muke neman mafita ga ciwon daji da ya harbi jam’iyyarmu ta PDP; ba mu sani ba ko ainihin ciwon daji ne ko a’a.”
Gwamna Abba ya gana da Shekarau
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙara kaimi wajen ganin ya dawo da tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau, cikin jam’iyyar APC.
Wani rahoto ya bayyana cewa gwamnan ya gana da Shekarau a Abuja kafin ya dawo Kano, a wani mataki na neman jawo shi cikin APC.
Majiyoyi sun bayyana cewa gwamnan na ƙoƙarin shimfiɗa dabaru tun da wuri domin tabbatar da cewa ya ci gaba da riƙe kujerarsa bayan zaɓen 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


