2027: Malamin Addini Ya Hango Halin da Tinubu Yake ciki kan Kashim Shettima
- Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashe kan shirye-shiryen zaben shekarar 2027 mai zuwa
- Primate Ayodele ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana cikin tsaka mai wuya kan batun yin takara tare da Kashim Shettima
- Babban faston ya nuna cewa duk zabin da Shugaba Tinubu ya yi wanda ya shafi Shettima, yana cike da matsala
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Jagoran cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya yi magana kan Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima.
Primate Ayodele ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu yana fuskantar wani babban ƙalubale na siyasa game da batun mataimakinsa, Kashim Shettima, gabanin babban zaɓen 2027.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa Primate Ayodele, ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ranar Laraba, 8 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito kan zargin Tinubu da haddasa rikicin ADC bayan hadewar Atiku, Obi da Kwankwaso
Me malamin addinin ya ce kan Bols Tinubu?
Babban faston ya yi iƙirarin cewa shugaban ƙasar ya tsinci kansa a wani yanayi mai sarkakiya kan Kashim Shettima.
Ya yi gargaɗin cewa ko dai ya ci gaba da amfani da Shettima a matsayin abokin takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC a 2027, ko kuma ya cire shi, duk suna tattare da mummunan sakamako ga siyasar sa.
“Cire Shettima da Tinubu zai yi ba zai haifar masa da ɗa mai ido ba, haka ma ci gaba da zama da shi ba zai amfane shi ba.”
“Yana cikin tsaka-mai-wuya, yana cikin sarkakiya, yana cikin ruɗani."
- Primate Ayodele
Ayodele: Za a matsa lamba ga Tinubu
Ayodele ya ƙara da cewa Tinubu na iya fuskantar matsin lamba daga abokan siyasa da masu ba shi shawara, waɗanda za su iya tura shi ga ɗaukar wannan tsauraran mataki kan kujerar mataimakin shugaban ƙasa.
“Mutane za su ba shi shawara. Kuma kusan ba zai yiwu ba a ce bai cire shi ba."
- Primate Ayodele

Source: Twitter
Matsalar da za a fuskanta kan Shettima
Ya ƙara da cewa ko da Tinubu ya yanke shawarar cire mataimakin nasa tare da ƙoƙarin shawo kan rikicin da hakan zai haifar, matakin zai bar tabon da zai yi wahalar warkewa, shafin worldnewsblog ya kawo maganar faston.
“Kuma wajen cire shi ɗin, babu yadda za ka yi ka lallashe shi wanda hakan zai sa ba zai yi masa ciwo ba."
- Primate Ayodele
Primate Ayodele ya dade yana yin jerin hasashe game da jiga-jigan siyasa da kuma abubuwan da ka iya faruwa a zaɓubbukan 2027, lamarin da ya sha tayar da muhawara.
Tinubu ya yaba wa Kashim Shettima
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kalaman yabo kan mataimakinsa, Kashim Shettima, a wajen taron majalisar tattalin arziki ta kasa (NEC).
Shugaba Tinubu ya bayyana mataimakin shugaban kasar na Najeriya, Kashim Shettima, a matsayin abokin tafiya na gari a tafiyar neman ci gaba.
Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da ake gudanarwa sun taimaka wajen daidaita tattalin arzikin kasar da kuma maido da amincewar kasashen duniya.
Asali: Legit.ng
