Bayan Yusuf Buhari, Dan Babban Sarki a Arewa zai Fito Takara a 2027
- Masu sha'awar tsayawa takara a zaben shekarar 2027 na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu a jihohi daban-daban yayin da lokacin siyasa ke kara karatowa
- 'Dan mai martaba Sarkin Daura a jihar Katsina, Muhammad Daha Umar Faruk ya ayyana niyyar yin takara a zaben 2027 da za a yi a badi
- Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan dan marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa zai yi takara a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Yayin da babban zaben shekarar 2027 ke kara karatowa, 'yan siyasa da sauran wadanda suke so a dama da su a Najeriya na kara shiri.
An samu rahoto da ya nuna cewa daya daga cikin 'ya'yan mai martaba Sarki Daura, Alhaji Umar Faruk Umar ya sanar da cewa zai yi takara.

Kara karanta wannan
Netanyahu ya fara shiga matsala a Isra'ila ana cigaba da yakar Iran da makwabtan kasashe

Source: Facebook
2027: Dan Sarkin Daura zai yi takara
Rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa bai nuna a wace jam'iyya Muhammad Daha Umar Faruk zai nemi takarar ba a halin yanzu.
Babban dan Sarkin Daura, Muhammad Daha Umar Faruk, ya ayyana aniyarsa a hukumance ta tsayawa takarar kujerar mazabar tarayya ta Baure/Zango a zaben 2027.
Faruk, wanda ke rike da sarautar gargajiya ta Danburam Daura, ya ce matakin da ya dauka ya biyo bayan kiraye-kirayen da yake samu daga jama’ar mazabarsa da ke bukatar ya wakilce su a Majalisar Tarayya.
“Ina so in sanar da dukkan magoya bayana cewa ni, Muhammad Daha Faruk, na yanke shawarar amsa kiran da suka yi,”
Inji shi.
Trust Radio ta wallafa cewa ya kara da cewa:
“Na amince zan tsaya takarar kujerar Majalisar Tarayya domin wakiltar mazabar Baure/Zango a zaben 2027.”
Gargadin da dan Sarkin Daura ya yi
Matashin basaraken ya kuma gargadi magoya bayansa da su guji kamfen din da ke dauke da cin zarafi, yana mai kira da su kiyaye mutunci yayin gudanar da harkokin siyasa.
Ya yi kira da cewa:
“Ina so in yi amfani da wannan dama in bukaci dukkan magoya bayana da su guji duk wani abu da zai kai ga cin zarafi ko raina wani da sunan goyon bayana,”

Source: Original
A wace jam'iyya zai yi takara?
Duk da har yanzu Faruk bai bayyana jam’iyyar da zai tsaya takara a karkashinta ba, masu lura da al’amura na ganin wannan na iya kasancewa wata dabarar siyasa.
Sai dai majiyoyi na kusa da shi sun nuna cewa yana iya shiga daya daga cikin jam’iyyun APC ko ADC a nan gaba kadan domin neman kujerar.
An nemi Yusuf Buhari ya yi takara
A wani rahoton, kun ji cewa wasu jagororin jam'iyyar APC a jihar Katsina sun nuna goyon baya ga Yusuf Buhari ya tsaya takarar majalisar wakilai.
Sun sanar da cewa gamsuwa da nitsuwar Yusuf Buhari da fatan alheri da ake masa ne ta sanya su neman ya fito takara domin kawo cigaba.
Haka zalika 'yan jam'iyyar sun nuna goyon bayansu ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina.
Asali: Legit.ng
