Kusa a APC Ya Fada wa Abba Wanda Zai ba Mataimakin Gwamna Ya Ci Zabe

Kusa a APC Ya Fada wa Abba Wanda Zai ba Mataimakin Gwamna Ya Ci Zabe

  • Jigon APC a Kano, Garba Kore Dawakin Kudu, ya shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zaɓi mataimaki mai jama’a domin nasarar 2027
  • Ya ce su aiki za su yi tsakani da Allah domin Abba ya koma kujerar gwamna, Abba sai ya dauki mai jama'a a dukkanin kananan hukumomi
  • Ya bayyana haka ne a lokacin da gwamnatin tarayya da majalisar dokokin Kano ke da zabinsu a kujerar, kuma an ci karo a wanda ake so

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kusa a jam’iyyar APC, Alhaji Garba Kore Dawakin Kudu ya shawarci gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da ya ɗauki mutumin da zai taimaka masa domin ya koma kujerar da yake kai a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala: Abubuwan da ya kamata a sani game da matashin da ke neman hana ruwa gudu a ADC

Garba Kore Dawakin Kudu ya bayyana cewa duk da lalacewar siyasa, akwai buƙatar a yi aiki da mutumin da ke da jama’a idan har ana son kai ga nasara.

Ana son Abba ha naɗa mai jama'a a matsayin mataimakin gwamna
Tsohon ɗan takarar mataimakin gwamna a Kano, Murtala Sule Garo da Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Murtala Sule Garo/Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A wata hira da APN Hausa ta yi da shi, wacce aka wallafa a shafin Facebook na kafar, Kore ya bayyana cewa babu wanda ya fi Murtala Sule Garo dacewa da abin da gwamnan ke buƙata a 2027.

Jigon APC ya shawarci Abba

A cewar Garba Kore, Murtala Sule Garo yana da mutanen da za su iya yin siyasa tare da shi saboda alherin da ya daɗe yana yi masu a ƙananan hukumomi 44 na jihar

A kalamansa:

"Yana daukan Murtala Sule Garo ya ba shi mataimaki, ya gama gyara rabin siyasarsa. Mu aiki ne a gabanmu, aiki za mu yi."
"Komai lalacewar siyasa, sai ka yi da mai mutane. Komai lalacewar siyasa, sai ka dauko mai albarkar mutane ka yi da shi."
"Ai ba da surutu ake cin zabe ba, da mu'amala ake cin zabe."

Ya ƙara da cewa siyasa na buƙatar kusanci da jama’a da kuma kyakkyawar hulɗa, ba wai yawan magana kawai ba.

Kara karanta wannan

Tafiyar Gawuna ADC ta fara lahanta APC a Kano, shugaba a jam'iyya ya bi ubangidansa

Jigon APC ya nemi Falgore ya hakura

Alhaji Garba Kore ya bayyana cewa har makusantan Gwamna Abba Kabir Yusuf, ciki har da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore, sun amfana da irin tasirin Murtala Sule Garo.

Kore na ganin yaƙi sai da kwananda
Tsohon kwamishinan ma'aikatar kananan hukumomi a Kano Murtala Sule Garo Hoto: Murtala Sule Garo
Source: Facebook

A kalaman Garba Kore:

"Yanzu kamar Kakakin majalisa, ya fi kowa sanin ranar Murtala, ya fi kowa sanin Murtala ya fi shi jama'a."
"Ba shi ya ce zaɓe ba muka kwace. Kwace-kwacen nan mu ma mun yi ko?"
"Mu hada kai mu yi siyasa."

Kore ya kuma ba wa Shugaban Majalisar haƙuri, yana mai cewa lokaci ya yi da dukkan ‘yan APC za su haɗa kai domin cimma burin siyasa.

Ya jaddada cewa a halin yanzu, kowa a cikin APC na goyon bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana mai kira da a ajiye saɓani a gefe domin ci gaban jam’iyya da kuma nasarar zaɓe mai zuwa.

Abba na tsaka mai wuya a Kano

Kara karanta wannan

An kama mai suna 'John' cikin masu kai hari a kungiyar Boko Haram

A baya, mun wallafa cewa rikicin siyasa ya ƙara ƙamari kan naɗin Mataimakin gwamnan Kano bayan Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ya yi murabus.

Fadar Shugaban Ƙasa na goyon bayan a naɗa Murtala Garo, amma ‘yan majalisa na matsa wa domin a naɗa shugabansu, Rt. Hon. Jibrin Isma'il Falgore.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na cikin matsin lamba daga ɓangarori daban-daban domin ya nada wanda suke so a matsayin mataimakin gwamna gabanin zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng