Siyasar 2027: Atiku da Kwankwaso na cikin Matsala, ADC Ta Sake Darewa Gida 2

Siyasar 2027: Atiku da Kwankwaso na cikin Matsala, ADC Ta Sake Darewa Gida 2

  • Rikicin jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ya kara tsananta bayan bullowar sabon bangare ana shirin zaben 2027
  • Sabon tsagin ya nesanta kansa daga bangaren David Mark da Nafiu Bala wanda ake ta yin rigima kan shugabancin ADC
  • Don Norman Obinna ya ce su ne sahihan shugabannin jam’iyyar, wacce yan adawa suka cika domin kifar da gwamnatin APC

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rikicin da ke addabar jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC) ya dauki sabon salo ana shirin zaben 2027.

Hakan ya biyo bayan bullowar wani sabon tsagi a cikin jam’iyyar wanda David Mark ya ke jagoranta da hukumar INEC ta ce ba ta san da shi ba.

An sake samun baraka a jam'iyyar ADC
Sabon shugaban tsagin ADC a Najeriya, Don Norman Obinna. Hoto: @Imranmuhdz.
Source: Twitter

Sabon tsagin ya bayyana cewa ba ya goyon bayan bangaren David Mark ko na Nafiu Bala, yana mai cewa yana wakiltar sahihan shugabannin jam’iyyar, cewar AIT News.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito kan zargin Tinubu da haddasa rikicin ADC bayan hadewar Atiku, Obi da Kwankwaso

An sake samun sabon 'shugaban' jam'iyyar ADC

Jagoran sabon bangaren, Don Norman Obinna, ya yi ikirarin cewa su ne halastattun mambobin kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da aka zaba.

Rahotanni sun nuna cewa bangaren ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja.

An kuma ce wa’adin tsohon shugaban jam’iyyar, Ralph Nwosu, ya kare tun a watan Agustan 2022 kafin ya mika shugabanci ga bangaren David Mark.

Majiyoyi sun kara da cewa Nwosu ya fuskanci kararraki da dama a kotu saboda kin sauka daga mukaminsa.

A cewar majiyoyi, bangaren da Don Norman Obinna ke jagoranta ya yi ikirarin cewa shi ne sahihin kwamitin zartarwa na kasa na jam’iyyar.

Bangaren ya ce ya dauki matakin shiga domin tafiyar da harkokin jam’iyyar kafin babban taron kasa na gaba, cewar rahoton Punch.

Obinna ya ce:

“Wa’adin Ralph Nwosu, wanda ya mika jam’iyyar ga bangaren David Mark, ya kare tun a watan Agustan 2022, sannan daga baya ya fuskanci jerin kararraki saboda kin sauka daga mukaminsa.”

Kara karanta wannan

An gano jam'iyyu 2 da Atiku, Kwankwaso za su iya komawa saboda tsaro kafin 2027

Rikici ya sake ballewa a ADC
Shugaban ADC, David Mark, Nafiu Bala da Atiku Abubakar. Hoto: David Mark/ Nafiu Bala /@atiku.
Source: Twitter

An fayyace matsayin Nafiu Bala a ADC

Wannan sabon rikici na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun sabani a cikin jam’iyyar, wanda ke kara jefa makomar ADC cikin rashin tabbas.

Tsagin ya kuma fayyace matsayin Nafiu Bala, inda ya ce matashin bai ma taba rike mukamin mataimakin shugaban jam'iyyar ba kamar yadda ya ke ikirari.

Ya kara da cewa:

“Bai taba rike mukamin mataimakin shugaban jam’iyyar ADC mai adawa ba,”

Har ila yau, tsagin Obinna ya tabbatar da cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na ADC, Dumebi Kachikwu, har yanzu mamba ne a jam’iyyar.

Rikicin ADC zai jawo matsala ga Atiku, Kwankwaso

A baya, mun ba ku labarin cewa wasu rahotanni sun nuna cewa Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na shirin barin ADC gabanin zaben 2027.

Rikicin shugabanci da matakin INEC ya jefa ADC cikin rudani mai tsanani wanda ake fargabar zai iya jawo mata asara a zaben.

Majiyoyi sun ce yan siyasar na duba yiwuwar komawa jam’iyyu biyu a matsayin mafita domin gudun ka da lokaci ya kure masu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.