Siyasar Kano Za Ta Sauya Salo bayan Ganawar Shekarau da Tinubu, Abba Kabir
- Tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya gana da shugaban kasa, Bola Tinubu a jihar Lagos
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa Shekarau na shirin komawa APC gabanin zaben shekarar 2027 da ake tunkara
- Rikicin siyasar Kano na kara tsananta bayan sauye-sauyen jam’iyyu da Rabiu Kwankwaso da Abba Kabir suka yi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau, na dab da kammala shawarwari domin komawa jam’iyyar APC gabanin babban zaben 2027.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon ministan ilimi ya yanke wannan shawara ne bayan ganawa daban-daban da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Source: Facebook
Rahoton The Guardian ya ce tsohon gwamnan jihar ya kuma gana da gwamna Abba Kabir Yusuf yayin da ake shirin zaben 2027.
Shekarau ya gana da Tinubu a Lagos
An ruwaito cewa Shekarau ya gana da Tinubu a Lagos lokacin hutun Easter domin tattauna yadda za a karfafa APC a Kano.
Haka kuma, Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da shugaban APC na Kano, Umar Haruna Doguwa, da kwamishinan sufuri, Haruna Isa Dederi, sun ziyarci Shekarau a gidansa domin jawo shi APC.
Wani rahoto ya bayyana cewa gwamnan ya gana da Shekarau a Abuja kafin ya dawo Kano, a wani mataki na neman jawo shi cikin APC.
Wata majiya kusa da Shekarau ta tabbatar da ganawar, tana mai cewa tana daga cikin shawarwari da ake yi domin lallashin tsohon gwamnan ya koma APC, cewar Tribune.

Source: Facebook
Ganawar da Kwankwaso ya yi da Shekarau
Ziyarar ta zo ne makonni biyu bayan Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da Shekarau yana kokarin jawo shi zuwa ADC.
Sai dai Kwankwaso ya samu nasarar jawo tsohon mataimakin gwamna, Nasiru Yusuf Gawuna, wanda ya koma ADC bayan ya bar mukaminsa na gwamnatin tarayya.
A watan Fabrairun shekarar 2026 ne siyasar Kano ta rikice bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya rabu da Kwankwaso domin karbe iko da tsarin siyasa, sakamakon rikicin NNPP.
Duk da suka daga wasu magoya bayan Kwankwasiyya, daga baya Kwankwaso ma ya bar NNPP zuwa ADC domin karfafa jam’iyyarsa.
Shekarau ya taba kare matakin Abba Kabir Yusuf na sauya sheka, yana cewa hakan ya yi daidai da abin da Kwankwaso ya taba yi a baya.
Mai magana da yawun Shekarau, Sule Yau Sule, ya ce har yanzu ana shawarwari, kuma za a sanar da mataki na gaba nan gaba.
Har yanzu ana sa ido da kuma dakon ganin wace jam'iyya ce Shekarau zai koma duk da cewa alamu sun nuna cewa ya karkata zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Kano da Najeriya.
Shekarau ya magantu kan kifar da Tinubu
A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya fayyace kalamansa kan hadakar 'yan adawa.
Shekarau ya bayyana cewa hadakar daidaikun mutane ba ta jam'iyyu ba, ba za ta iya raba Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mulki ba a 2027.
Ya kawo misalin yadda suka koyi darasi a baya bayan sun yi yunkurin kafa hadaka don kifar da Goodluck Jonathan a shekarar 2011.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

