Gaskiya Ta Fito kan Zargin Tinubu da Haddasa Rikicin ADC bayan Hadewar Atiku, Obi da Kwankwaso
- Fadar shugaban kasa ta musanta jita-jitar cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya kunno wa jam'iyyar hadaka, ADC wuta gabanin 2027
- Mai magana da yawun shugaban, Bayo Onanuga ya ce wannan jita-jita ba gaskiya ba ne domin babu ruwan Tinubu da harkokin ADC
- Ya kuma soki tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi da magoya bayansa, yana mai cewa sun gaza warware rikicin LP balle kuma na ADC
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Fadar shugaban kasa ta musanta rade-radin da ake yadawa cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya haddasa rigingimun cikin gida da suka addabi ADC.
Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasa, ya bayyana cewa Tinubu ba shi da hannu a cikin rikicin shugabancin da ke addabar ADC da yan adawa suka yi hadaka.

Source: Twitter
Hakan na kunahe a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, mai taken “Martani na ga mutanen Peter Obi."
Onanuga ya soki magoya bayan Obi
Onanuga ya ce ba daidai ba ne ga wasu ‘yan siyasa su mayar da Tinubu “kamar juji” (wato wanda ake jinga wa kowane tarkace) kan matsalolin siyasa da su da kansu suka tafka.
“Ina mamakin dalilin da ya sa wadannan ‘yan siyasa marasa kishin kasa suke mayar da Shugaba Bola Tinubu kamar juji, kowace bola suka kwaso su yaba masa."
“Shugaban kasa ba shi da wata alaka da batun watsar da jam’iyyar LP da Obi ya yi, ko kuma rudanin da ya tsinci kansa a ciki a jam’iyyar ADC."
- Bayo Onanuga.
Ya ce Obi ya kasa nuna bajintar jagoranci wajen warware rikicin cikin gida na LP, inda ya kara da cewa tsohon gwamnan na Anambra ya gwammace ya dogara da magoya bayansa na tafiyar Obidient maimakon gina tsarin siyasa mai karfi.
Shin Tinubu na da hannu a rikicin ADC?
Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce Obi ya shiga jam’iyyar ADC ne saboda yana bukatar tsarin siyasa da ke akwai domin cimma burinsa na zama shugaban kasa.
Haka kuma Onanuga ya yi zargin cewa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ne ya mallaki jam’iyyar ADC, inda ya jaddada cewa babu hannun Tinubu a rikicin ADC.
“Mene ne alakar Tinubu da rikicin ADC? Babu ko daya. Duk wata matsala da suke da ita, su suka jawo wa kansu,” in ji shi.

Source: Twitter
Ononuga ya ba Peter Obi mafita
Ya ce ya kamata Obi da abokan tafiyarsa su mayar da hankali wajen warware matsalolin da ke cikin jam’iyyarsu, ba zargin wanda ba shi da laifi na.
A rahoton The Cable, Onanuga ya ce:
“Ya kamata Obi da abokan tafiyarsa su gyara dabi’unsu, su kwashe dattin da ke cikin sabuwar jam’iyyarsu, sannan su yi takara don neman tikitin shugaban kasa. Su je su sasanta da Nafiu Gombe da sauran mambobin ADC.
A 'yan kwanakin nan an ga yadda Bayo Onanuga yake amfani da shafinsa na X wajen bada kariya ga Nafiu Bala wanda ake zargin yana neman kawo wa ADC matsala.
A matsayinsa na hadimin shugaban kasa, tsohon 'dan jaridar ya yi ta tsoma baki a rikicin cikin gidan jam'iyyar hamayyar, har ta kai wasu suna ganin da walakin.
Idan an duba shafinsa, za a ga wasu lokuta ya rika maida wa ADC martani da wani raddi da jam'iyyar APC ta yi mata.
ADC ta zargi INEC ta shirya mata makirci
A wani labarin, kun ji cewa ADC ta zargi hukumar INEC da kitsa abin da ta kira "tarko" da nufin hana jam’iyyar gabatar da ’yan takara a babban zaɓen 2027.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai zafi da sakataren yaɗa labarai na ADC a kasa, Bolaji Abdullahi ya fitar a jiya Litinin, 6 ga watan Afrilun 2026.
Jam’iyyar ADC ta yi zargin cewa matakan baya-bayan nan na INEC na iya fitar da ita daga tsarin zaɓen 2027 baki ɗaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


