2027: Atiku Ya Shiga Yarjejeniya da Kamfanin Kamun Kafa a Amurka a kan N1.9bn

2027: Atiku Ya Shiga Yarjejeniya da Kamfanin Kamun Kafa a Amurka a kan N1.9bn

  • Atiku Abubakar ya rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar Dala miliyan 1.2 da kamfanin kamun kafa na Amurka
  • Yarjejeniyar na da nufin ƙarfafa sunansa da dangantakarsa da hukumomin Amurka kafin zaɓen 2027 da za a yi a Najeriya
  • Ana ganin matakin na da alaƙa da fafatawar tikitin shugaban ƙasa a jam’iyyar hamayya ta ADC da za a yi nan gaba kaɗan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya kulla yarjejeniya ta Dala miliyan 1.2, kimanin Naira biliyan 1.9 da wani kamfanin kamun kafa da ke Amurka.

Ana ganin ya shiga wannan yarjejeniya mai tsadar gaske ne domin ƙarfafa matsayinsa a harkokin siyasa kafin zaɓen 2027 da za a buga a Najeriya.

Kara karanta wannan

Matakin INEC game da shugabannin ADC ya tafi gaban Trump da majalisar Amurka

Atiku ya shiga yarjejeniya da kamfanin Amurka
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar a wajen taro Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa takardun da aka miƙa wa Ma’aikatar SHARI’A ta Amurka sun nuna cewa Atiku ya ɗauki kamfanin Von Batten-Montague-York, L.C. da ke birnin Washington domin wannan aiki.

Atiku ya shiga yarjejeniya da kamfanin Amurka

Jaridar Punch t wallafa cewa Atiku ya dauki kamfanin aiki a karkashin yarjejeniya ta watanni 12 wacce aka sanya hannu a ranar 10 ga Maris, 2026 sannan aka yi rajista a ƙarƙashin dokar FARA a ranar 1 ga Afrilu, 2026.

A cewar bayanan, kamfanin zai ba da shawarwari na dabaru, hulɗa da majalisar dokoki da bangaren zartarwa na Amurka, da kuma kula da yadda ake kallon Atiku a idanun masu tsara manufofi da cibiyoyin gwamnati.

Atiku, wanda ya rike mukamin mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007, ya sha neman kujerar shugaban ƙasa a lokuta da dama amma Allah bai ba shi ba.

Atiku: Neman takarar Shugaban ƙasa ya yi zafi

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin sake fasalin siyasa gabanin zaɓen 2027, inda jam’iyyar hamayya ta ADC ke zama wata babbar dandalin haɗaka.

Kara karanta wannan

EFCC za ta jika wa Malami aiki, ta jero kadarori kusan 60 da ake so kotu ta kwace

Atiku ya shiga yarjejeniyar ana shirin neman tikitin takara a ADC
Peter Obi da Atiku Abubakar da ake sa ran za su nemi tikitin takarar shugaban kasa a 2027 Hoto: Atiku Abubakar
Source: UGC

A karkashin yarjejeniyar, kamfanin zai taimaka wajen sanar da jami’an gwamnatin Amurka kan batutuwan da suka shafi Najeriya, daga ciki har da dimokuraɗiyya, zaman lafiya a yankuna, ci gaban tattalin arziki, da hulɗar ƙasashen biyu.

Haka kuma, ana sa ran kamfanin zai taimaka wajen tsara saƙonnin manufofin Atiku, shirya ganawa da jami’an Amurka, da kuma inganta yadda ake kallonsa a Washington.

Yarjejeniyar ta bayyana manyan manufofi guda huɗu: ƙara fahimtar hangen nesa na shugabancinsa, ƙarfafa sunansa a Amurka.

Kamfanin zai kuma mayar da martani kan zarge-zargen gwamnati mai ci, da kuma gina alaƙa mai ƙarfi da cibiyoyin Amurka.

Rahotanni sun nuna cewa wannan shiri na da nasaba da fafatawar neman tikitin shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, inda ake sa ran Atiku zai kara da Peter Obi.

ADC: Kamfani zai kai karar INEC Amurka

A wani labarin, mun wallafa cewa kamfanin Amurka ya shirya tattaunawa da Shugaban kasa Donald Trump kan matakin INEC game da shugabancin jam'iyyar ADC.

Kara karanta wannan

INEC ta goge sunayen shugabannin ADC, tafiyar hadaka za ta iya rushewa

Hukumar zaben Najeriya ta INEC ta dakatar da amincewa da shugabancin ADC, abin da ya jawo damuwa kan sahihancin zabe mai zuwa, lamarin da ake kallo a matsayin barazana.

Kamfanin ya bukaci shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da an yi sahihin zabe da zai nuna ra’ayin ‘yan Najeriya da wanda za su jefa wa kuri'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng