Rigima Ta Farraƙa APC kan Takarar Yusuf Buhari, an Ja Layi tsakanin Ƴan Jam'iyya

Rigima Ta Farraƙa APC kan Takarar Yusuf Buhari, an Ja Layi tsakanin Ƴan Jam'iyya

  • Rikici ya barke a cikin jam’iyyar APC a Daura bayan wasu ‘yan jam’iyya sun amince da takarar Yusuf Buhari
  • Hakan ya biyo bayan amincewa da dan marigayi Muhammadu Buhari a matsayin ɗan takara a majalisar wakilai daga jihar Katsina
  • Wasu manyan jiga-jigan APC daga ƙananan hukumomi biyar sun yi fatali da zargin ɗora ‘yan takara, suna cewa ba za su amince da hakan ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Daura, Katsina - Rigima ta barke kwanaki kaɗan bayan wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a Katsina sun amince da Yusuf Buhari ya yi takara.

Wasu yan APC sun amince dan marigayi Muhammadu Buhari ya tsaya takara kujerar majalisar tarayya daga jihar Katsina.

An samu rikici a APC kan amincewa da takarar Yusuf Buhari
Yusuf Buhari da mahaifinsa marigayi Muhammadu Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Twitter

Rigima ta kunno kai a jam'iyyar APC

Rahoton Daily Trust ya tabbatar da cewa rikici ya ɓarke a Daura tsakanin shugabannin jam’iyyar kan lamarin.

Kara karanta wannan

An gano jam'iyyu 2 da Atiku, Kwankwaso za su iya komawa saboda tsaro kafin 2027

A wani taro da aka gudanar a Sandamu makon jiya, wata ƙungiya ta ayyana Yusuf Buhari a matsayin wanda suka fi so ya tsaya takarar majalisar wakilai ta Daura, Sandamu da Mai’adua.

Shugaban ƙaramar hukuma, Usman Na Lado, ya bayyana cewa wannan matsaya ta samo asali ne daga yarjejeniya tsakanin jiga-jigan jam’iyyar domin ƙarfafa damar APC a zaɓe.

Ya ƙara da cewa sun zaɓi Yusuf Buhari ne bisa la’akari da ƙwarewarsa da karɓuwar da yake da ita a cikin ‘yan jam’iyyar a yankin.

Lado ya kuma ambaci Shugaba Bola Tinubu da gwamna Dikko Radda a matsayin ‘yan takarar APC na shugaban ƙasa da gwamna a zaɓen 2027.

Wasu sun bukaci Yusuf Buhari ya yi takara a Katsina
Yusuf Buhari yayin wani taro a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Haka kuma ya bayyana cewa sun goyi bayan shugaban majalisar dokokin Katsina, Nasiru Yahaya Daura, domin ya tsaya takarar sanatan Daura a zaɓe mai zuwa.

Yan APC sun ki amincewa da Yusuf Buhari

Sai dai bayan wani taro na daban a ƙarshen mako, wasu manyan jiga-jigan APC daga ƙananan hukumomi biyar sun yi alƙawarin adawa da ɗora ‘yan takara.

Sun zargi wasu masu riƙe da muƙaman gwamnati da yin aiki ba tare da shawarar kowa ba, suna jingina hakan ga gwamna domin yaudara ga jama’a.

Kara karanta wannan

Tafiyar Gawuna ADC ta fara lahanta APC a Kano, shugaba a jam'iyya ya bi ubangidansa

Shugaban ƙaramar hukumar Daura, Bala Musa Daura, ya buƙaci jama’a su yi watsi da rahotannin da ke cewa an riga an ɗora wasu ‘yan takara, cewar BusinessDay.

Haka zalika mai ba gwamna shawara kan harkokin siyasa, Yau Umar Gwajo-Gwajo, ya tabbatar da cewa gwamna bai bayar da irin wannan umarni ba.

'Yan majalisa na neman takara a APC

A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan majalisar wakilai da gwamnonin jam'iyyar APC sun fara neman tikitin takarar 2027 ba tare da zaben fitar da gwani ba.

Rahotanni sun nuna cewa wasu gwamnoni da wa'adin su zai kare sun fara shirin neman kujerun da 'yan majalisar ke rike da su a yanzuu.

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum sun fara kira ga APC da ta yi taka tsan-tsan wajen ba 'yan takara tikiti domin kaucewa rikici.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.