Jagora a APC, Danbilki Kwamanda Ya Faɗi Wanda zai Ci Zaɓen Kano a 2027
- Jagora a APC reshen Kano, AbdulMajeed Danbilki Kwamanda ya ce Sanata Rabiu Kwankwaso zai ƙarfafa ADC
- Ya gargaɗi masu amfani da karfi a siyasa, yana cewa ba a tilasta wa jama'a bin wani dan siyasa ta ƙarfi da yaji
- Ya yi zargin gwamnatin Kano ta hana wasu muhimman ababen more rayuwa saboda haka za su hakura da zaɓen APC a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano –Fitaccen ɗan jam’iyyar APC, AbdulMajeed Danbilki Kwamanda, ya bayyana cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai busa wa jam’iyyar ADC rai a jihar Kano.
Ya bayyana hakan ne yayin da Sanata Kwankwaso ya yanke katin zama cikakken ɗan jam’iyyar ADC a Kano, gabanin zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.

Source: Twitter
A wata tattaunawa da DC Hausa ta wallafa a shafinta na Facebook, Danbilki Kwamanda ya ja kunnen masu niyyar amfani da karfi a kan jama’a, yana mai cewa babu dabara an siyasar tilas ko danniya ba.
Jigon APC ya magantu kan siyasar Kano
Danbilki Kwamanda ya ƙara da cewa, manufar siyasa ita ce taimaka wa al’umma wajen samun ilimi, ruwan sha da sauran muhimman abubuwan more rayuwa.
Ya ce:
"Siyasa a yi ta ba da gaba ba, ba da cin mutunci ba. Idan kana son mutum, to kana don mutum. Amma a ce sai an hada da wasu jami'an tsaro an tilasta ka a ce sai ka bi mutum, wannan ba siyasa ba ce."
"Siyasa ba a mata dole. Ko lokacin jahiliyya, lokacin NEPU da NPC da aka yi wannan, su kansu sun gane kuskure ne."
Danbilki Kwamanda ya kuma shawarci jama’a da su guji cin mutunci a harkar siyasa, yana mai cewa iko yana hannun Allah SWT, kuma yana iya ba wa kowa a kowane lokaci.

Kara karanta wannan
"Mun san Kwankwaso ba kanwar lasa ba ne": Jagora a APC ya ce suna shirin karo da Madugu
Kwankwaso zai fitar da gwamna - Danbilki Kwamanda
A cewarsa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yana da tasiri sosai a siyasar Kano, inda ya taka rawa wajen kafa gwamnatocin da suka gabata.
Ya ce Kwankwaso ne ya taimaka wajen kafa gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da kuma ta Abba Kabir Yusuf a jihar, kuma yanzu wani dan ADC zai samu.

Source: Twitter
Ya ƙara da cewa:
"Zai busa wa ADC rai a jihar Kano."
"Shi yasa kullum na ke cewa za mu yi gini iya linta, amma ba za mu yi gini mu sa dekin ba."
"Gwamnatin jiha, duk wanda Kwankwaso ya tsayar shi za mu yi."
Sai dai Danbilki Kwamanda ya yi zargin cewa gwamnatin Kano ta hana wasu mutane muhimman abubuwan more rayuwa kamar ruwan sha, magunguna da sauran kayan tallafi.
Ya jaddada cewa dole ne a samu sauyin gwamnati a jihar Kano, duk da cewa sun shirya ci gaba da mara wa APC baya a zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisu a shekarar 2027.
Kwankwaso butulu ne –Danbilki Kwamanda
A baya, kun ji cewa wani jigo siyasar Kano, Dan Bilki Kwamanda, ya ce nan ba da dadewa ba za su kawo karshen siyasar jagoran NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwamanda ya ce yayi mamakin yadda har Tinubu ya tsorata da Kwankwaso, wanda a cewar sa shi Kwankwaso 'duba gari ne' wanda bai kamata aji tsoron sa ba ko kadan.
Da ya ke tsokaci kan furucin Dan Bilki Kwamanda, wani Isma'il Sarkin Tafiya, a Dawakin Tofa da ke jihar Kano, ya ce bai kamata a bar ire-iren Kwamandan suna yawo a gari ba.
Asali: Legit.ng

