Amsar APC ga Gwamnoni, Yan Majalisa da ke Neman Tikitin Takara Kai Tsaye a 2027

Amsar APC ga Gwamnoni, Yan Majalisa da ke Neman Tikitin Takara Kai Tsaye a 2027

  • Jam’iyyar APC ta yi karin haske kan jita-jitar da ake yadawa game da tikitin takara ga wasu yan siyasa a kasar
  • APC ta yi magana ne kan rahoton cewa za ta ba gwamnoni da ‘yan majalisa tikitin kai tsaye a zaben 2027
  • Mataimakin shugaban APC na kasa (Kudu), Ben Nwoye, ya ce tsarin tikitin kai tsaye ba ya cikin kundin tsarin jam’iyya ko doka, kuma dole a bi ka’ida

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam’iyyar APC ta fayyace gaskiya kan jita-jitar cewa tana shirin bai wa gwamnoni da ‘yan majalisa tikitin kai tsaye.

Jam'iyyar APC ta musanta labarin tana mai cewa dole duk masu neman takara su shiga zaben fidda gwani.

APC ta yi magana kan tikiti ga yan takara a 2027
Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Nentawe Yilwatda. Hoto: All Progresssives Congress.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata hira da gidan talabijin na Arise News ya yi da mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa (Kudu), Ben Nwoye.

Kara karanta wannan

"Bai son zabe": Melaye ya fallasa abin da Tinubu yake so kan zaben 2027

APC ta ki amincewa da bukatar gwamnoni, yan majalisa

Nwoye ya bayyana cewa wannan tsarin ba ya cikin kundin dokokin jam’iyyar kuma za a bi hanyar da ta dace ne.

Ya ce kundin tsarin ya tanadi cewa duk bayan shekaru hudu, gwamna ko dan majalisar kasa ko ta jiha dole ya koma wajen mazabarsa domin sake neman amincewar jama’a.

Nwoye ya jaddada cewa dokar zabe ta tanadi yin zaben fidda gwani, inda ya ce akwai hanyoyi biyu, ko dai yarjejeniya ko kuma kuri’a.

Ya ce yarjejeniya tana cikin tsarin jam’iyya APC kuma doka ta amince da ita, amma abin da ba a sani ba a kundin tsarin shi ne batun tikitin kai tsaye.

Ya kara da cewa rahotannin da ke cewa an nemi tikitin kai tsaye ko an tattauna hakan a tarukan jam’iyya ba gaskiya ba ne, kuma an wuce gona da iri.

APC ta karyata shirin ba gwamnoni, yan majalisa tikiti kai tsaye
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin halartar liyafar cin abinci a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Wane shiri APC ke yi kan zaben fitar gwani?

A cewarsa, ko da masu rike da mukamai suna aiki yadda ya kamata, dole ne su gabatar da rahoton ayyukansu ga jama’a domin su yanke hukunci.

Kara karanta wannan

APC na shan matsin lamba kan takarar 2027, an yi gargadin rikici zai barke

Ya bayyana cewa idan dan majalisa ko gwamna bai yi abin da ya kamata ba, to masu kada kuri’a ne za su tantance ko ya cancanci dawowa kan kujerarsa.

Nwoye ya kuma ce har yanzu APC ba ta fitar da jadawalin zaben fidda gwani ba, duk da cewa INEC ta nuna cewa za a iya fara daga ranar 23 ga wannan wata.

Ya kara da cewa jam’iyyar ba ta fara sayar da fom din takara ba, yana mai cewa ana yada bayanan da ba su da tushe kan batun tikitin kai tsaye.

An gargadi APC kan tikiti kai tsaye

Mun ba ku labarin cewa jagororin jam'iyyar APC da suka hada da gwamnoni da 'yan majalisa na neman a ba su tikitin takara kai tsaye ba tare da zaben fitar da gwani ba.

Masu jan ragamar APC sun nuna bukatar hakan ne yayin da 'yan siyasa da jam'iyyu suka fara shirye-shiryen siyasar 2027 da ta ke daukar hankali a yanzu.

Wani mai sharhi kan lamuran siyasa, Mathew Ifeolu ya bayyana cewa bukatar gwamnoni da 'yan majalisun za ta iya haifar da babban rikici a APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.