NNPP Ta Fadi Zunubin Kwankwaso a Siyasa, Ta Tausayawa Jam'iyyar ADC
- Jam'iyyar NNPP ta yi tsokaci kan rikicin shugabanci da ya addabi takwararta ta ADC mai adawa a Najeriya
- NNPP ta bayyana cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a 2023, Rabiu Musa Kwankwaso na da hannu a rikicin da ya addabi ADC
- Ta nuna cewa zunuban da Kwankwaso ya aikata a siyasa ne suka sanya ADC ba ta zaune lafiya ta ke fama da rikici
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Jam’iyyar NNPP mai adawa ta yi magana kan rikicin da ya addabi hadakar 'yan adawa ta ADC.
Jam'iyyar NNPP ta ɗora alhakin rikicin shugabanci da ke addabar ADC a wuyan tsohon ɗan takararta na shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na ƙasa, Ogini Olaposi, ya fitar a ranar Alhamis, 2 ga watan Afirilun 2026 a Legas.
Hakan na zuwa ne yayin da jam’iyyar NNPP ta nuna tausayinta ga ADC kan ƙalubalen da take fuskanta.
Me NNPP ta ce kan rikicin ADC?
NNPP ta ce "ba ta yi mamaki ba" da wannan ci gaba, tana mai zargin cewa lamarin sakamakon ayyukan Kwankwaso ne da Buba Galadima.
Ogini Olaposi da 'yan bangarensa sun samu sabani da Kwankwaso har aka barka NNPP zuwa gida biyu.
Wannan martani ya biyo bayan sanarwar da hukumar INEC ta yi na janye amincewa da shugabancin ADC, ciki har da David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakatare.
Jam'iyyar NNPP ta fadi laifin Kwankwaso
“Ba mu yi mamakin ganin cewa shugabannin ADC ba su sani ba cewa Allah yana fushi da Kwankwaso da Buba Galadima kan yunƙurin da suka yi na ƙwace NNPP ta bayan fage."
"Babban laifin da suka yi wa Allah shi ne sauya tambarin asali da launin jam’iyyar NNPP ba tare da amincewar jam’iyyar ba.”
"An yi rajistar NNPP ne tun a shekarar 2001, yayin da Kwankwaso da Buba Galadima da sauran mambobin tafiyar Kwankwasiyya suka shigo ne kawai a shekarar 2022 kyauta domin tsayawa takarar shugaban ƙasa da sauran muƙamai a 2023.”
“Kwankwaso ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa, yayin da mabiya bayansa suka yi nasarar lashe zaɓen gwamna a jihar Kano da sauran muƙamai a matakin jiha da na majalisar tarayya.”
“Allah yana fushi da ADC saboda karɓar Kwankwaso da mabiyansa ba tare da ya je ya ba mambobin NNPP da shugabancinta haƙuri ba.”
- Ogini Olaposi
NNPP ta wanke APC, INEC daga zargi
Jam’iyyar ta bayyana lamarin a matsayin "abin baƙin ciki," tana mai ƙara da cewa ya kamata ADC ta fahimci cewa APC da INEC ba su da hannu a cikin halin da take ciki.
“ADC ba ta da wani dalili na goyon bayan dabi'ar cin amana, domin ba za ta iya iƙirarin rashin sanin abin da Kwankwaso da Buba Galadima suka yi wa NNPP ba, waɗanda suka kyautata musu a lokacin da suke cikin buƙata."
- Ogini Olaposi

Source: Facebook
Wace shawara NNPP ta ba ADC?
NNPP ta shawarci ADC da ta umarci Kwankwaso da Buba Galadima su je su nemi afuwar abin da suka aikata.
“ADC ta umarci Kwankwaso da Galadima su je su nemi afuwar mambobin NNPP da shugabancinta, sannan su yi sulhu, su nemi gafarar Allah don gaba.”
“Ba wani abu ba ne ko har yanzu suna cikin NNPP ko a’a; idan sun gaza yin hakan, fushin Allah zai ci gaba da shafar su."
- Ogini Olaposi
ADC ta bukaci shugaban INEC ya yi murabus
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban jam'iyyar ADC na kasa, Sanata David Mark, ya bukaci shugaban iNEC, Farfesa Joash Amupitan, ya yi murabus.
Sanata David Mark, wanda yake tsohon shugaban majalisar dattawa ne, ya ce jam'iyyar ba ta da sauran kwarin gwiwa kan INEC.
Hakazalika, ya bukaci 'yan Najeriya da su yi jayayya da yunkurin da ake yi na mayar da Najeriya karkashin tsarin jam'iyya daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


