"Bai Son Zabe": Melaye Ya Fallasa Abin da Tinubu Yake So kan Zaben 2027

"Bai Son Zabe": Melaye Ya Fallasa Abin da Tinubu Yake So kan Zaben 2027

  • Tsohon sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Sanata Dino Melaye, ya yi tsokaci kan zaben shekarar 2027 da ake tunkara
  • Sanata Dino Melaye ya yi zargi kan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu dangane da zaben wanda aka fara shirye-shirye a kansa
  • Melaye ya kuma nuna cewa jam'iyyar APC ta shiga dimuwa kan farin jinin da hadakar 'yan adawa ta ADC take kara samu

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma kuma jigo a jam’iyyar ADC, Dino Melaye, ya yi zargi kan Shugaba Bola Tinubu.

Dino Melaye ya ce Tinubu da cewa ba shi da sha’awar yin takara ta dimokuraɗiyya a zaɓen 2027, maimakon haka yana neman abin da ya kira "naɗin sarauta" a matsayin shugaban ƙasa.

Melaye ya yi maganganu kan Tinubu
Sanata Dino Melaye da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Dino Melaye, Bayo Onanuga
Source: Facebook

Dino Melaye ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a ranar Alhamis, 2 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

An gano matsalar da ADC za ta samu da INEC kan takarar Shugaban kasa

Dino Melaye ya yi magana kan APC

Ya kuma zargi jam’iyyar APC mai mulki da shiga tsananin fargaba saboda ƙaruwar farin jinin haɗakar jam’iyyun adawa ta ADC.

Melaye ya yi iƙirarin cewa damuwar da jam’iyya mai mulki ke nunawa kan ADC ba kawai gaba ce ta siyasa ba, tana nuna barazana ce ga kimar dimokuraɗiyya a ƙasar.

Me Melaye ya ce kan Bola Tinubu?

Melaye ya yi zargin cewa Shugaba Tinubu ba ya sha’awar takara ta dimokuraɗiyya, illa dai wani tsari na siyasa inda ake riƙe madafun iko ta hanyar danniya.

“Shugaba Bola Tinubu naɗin sarauta yake so a yi masa; ba ya son zaɓe."

- Dino Melaye

A cewarsa, jam’iyyar APC ta nuna rashin jin daɗi a fili game da abin da ya kira "gagarumar ficewa" da ’yan siyasa da magoya baya ke yi daga wasu jam’iyyun zuwa ADC.

Melaye ya ce APC na shakkar ADC

Tsohon 'dan takarar gwamnan ya ce wannan ci gaba ya fallasa tsoron da jam’iyya mai mulki ke ciki duk da iƙirarin da take yi na ita ce ke da iko a ƙasar.

Kara karanta wannan

Bayan shigar Kwankwaso cikin jam'iyyar, ADC ta fallasa makarkashiyar da ake kulla mata

“APC ta fita hayyacinta. APC ta lura cewa ADC ita ce kaɗai jam’iyya a Jamhuriyar tarayyar Najeriya da za ta iya ƙalubalantar ta."
"Sun ga yadda ake kwarara daga wasu jam’iyyu zuwa ADC, kuma ni kaina ina mamakin yadda suke jin tsoro. Kuna cewa kuna da gwamnoni 32, to me ku ke tsoro?”

- Dino Melaye

Dino Melaye ya ce APC na tsoron ADC
Tsohon sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Dino Melaye Hoto: Dino Melaye
Source: Facebook

Melaye ya soki Shugaba Tinubu

Melaye ya kuma soki Shugaba Tinubu, inda ya zarge shi da nuna halayen da suka saɓa wa dimokuraɗiyya da kuma neman kafa tsarin mulkin danniya maimakon bari a yi sahihin zaɓe.

“Yana son mu koma tsarin mulkin masarauta, a koma ana cewa ‘kabiyesi’ (ranka ya daɗe) inda kawai za a yi musu naɗin sarauta.”

- Dino Melaye

Shugaban kasa Tinubu zai ziyarci Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyara zuwa birnin Jos na jihar Plateau.

Shugaba Tinubu zai ziyarci birnin Jos, babban birnin jihar Plateau, domin jajantawa gwamnati da al'umma kan hare-haren 'yan bindiga na baya-bayan nan da suka lakume rayukan bayin Allah.

Bayan kammala ziyarar ta'aziyya a Plateau, Shugaba Tinubu zai wuce birnin Legas domin gudanar da bukukuwan Good Friday.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng