Tinubu, Obi ko Atiku? Malaman Addini Sun Yi Hasashen Wanda Zai Lashe Zaben 2027

Tinubu, Obi ko Atiku? Malaman Addini Sun Yi Hasashen Wanda Zai Lashe Zaben 2027

  • Prophet Godwin Ikuru ya bayyana cewa duk da irin fafutukar da jam'iyyar ADC take yi, Shugaba Bola Tinubu ne zai sake yin nasara a 2027
  • Malamin addinin ya caccaki wasu 'yan siyasa da ya kira "masu wankiya" wadanda ke son kawo cikas ga gwamnatin APC gabanin zaben 2027
  • Wasu manyan Fastoci irin su Apostle Victor Oku da Pastor Emmanuel Ezeasor su ma sun gabatar da nasu hasashen wanda zai ci zabe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Lagos – Yayin da ake tunkarar babban zaben 2027, wasu shahararrun malaman addini a kasar nan sun fara fitar da hasashen abin da zai faru, inda akasari suka karkata ga nasarar Shugaba Bola Tinubu.

Prophet Godwin Ikuru, wanda shi ne wanda ya kafa cocin Jehovah Eye Salvation Ministry, ya bayyana cewa Ubangiji ya riga ya nuna masa nasarar Tinubu a zaben dake tafe.

Kara karanta wannan

2027: Jerin ministoci da manyan jami’an gwamnatin Tinubu 7 da suka yi murabus don takara

Malaman addinin Kirista sun hango nasarar Tinubu duk da kalubalen 'yan adawa
Hagu zuwa dama: Peter Obi, Atiku Abubakar, Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @PeterObi, @atiku, @officialABAT
Source: Twitter

Fastoci da suka hango nasarar Tinubu

Legit Hausa ta tattaro jerin manyan malaman addinin Kirista da suka yi hasashe kan zaben 2023:

1. Prophet Godwin Ikuru

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Prophet Ikuru ya bayyana cewa mutane da dama sun yi shakka a lokacin da ya yi hasashen nasarar Tinubu a 2023, amma abin ya tabbata.

Ya ce a 2027 ma, masu yi wa shugaban zagon kasa za su sha mamaki, domin kuwa, duk wani makircinsu ba zai iya kayar da gwamnatin APC ba.

"Haka abin zai faru a 2027. Kun dai yi tantama a kan hasashe na 2022 da 2023, kuma kun ga abin da ya faru. A 2027 ma, Ubangijin da ke tare da Asiwaju zai nuna wa 'yan adawa cewa su ba komai ba ne," in ji Prophet Ikuru.

Kalli bidiyon hasashen malamin a nan kasa:

Kara karanta wannan

Matashin da aka kama a Najeriya kan yakin Iran da Amurka ya fadi masu hannu a tsare shi

2. Apostle Victor Oku

Babban faston cocin Divine Mercy Church International, Apostle Victor Oku, ya bayyana cewa duk da irin hadakar da Atiku Abubakar, Peter Obi, da Rotimi Amaechi ke ginawa a inuwar ADC, Tinubu ne zai yi nasara.

Jaridar The Sun ta rahoto cewa, Apostle Oku, ya ce har yanzu Ubangiji yana tare da wannan gwamnati kuma mutum ba zai iya dakatar da abin da Ubangiji ya kaddara ba.

Malaman addinin Kirista sun hango nasarar Tinubu a zaben 2027.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a dakin taron majalisar zartarwa ta kasa da ke Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

3. Pastor Emmanuel Ezeasor

Shi ma Pastor Emmanuel Ezeasor ya bayyana a shafinsa na YouTube cewa jam'iyya mai mulki (APC) za ta yi dukkan abin da za ta iya domin tabbatar da cewa ta rike madafun iko a 2027.

Sai dai ya bukaci 'yan Najeriya da su kara kaimi wajen yin addu'a ga kasar, domin kakar zabe dake tafe za ta bukaci addu'o'i sosai domin samun zaman lafiya.

Kalli bidiyon malamin a nan kasa:

Kara karanta wannan

Lamari ya girma: Sanatan Amurka ya bankado 'sirrin' wasu manyan Najeriya

Malaman Musulunci sun taru don Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, malamai, 'yan siyasa da sarakuna sun taru a Abuja domin taya Shugaba Bola Tinubu murnar cika shekara 74 da haihuwa.

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da addu'o'i domin samun nasarar shugaba Bola Tinubu da cigaban Najeriya a wani taro a Abuja.

Fadar shugaban kasa ta sanar da cewa malaman addinin Musulunci da dama sun taru domin yi wa Tinubu addu'a, inda suka yi saukar Kur'ani sama da 100.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com