Wata Sabuwa: An Fara Shirin Tsayar da Yusuf Buhari Takara a Zaben 2027

Wata Sabuwa: An Fara Shirin Tsayar da Yusuf Buhari Takara a Zaben 2027

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Katsina sun nuna cewa an fara kira da a tsayar da dan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi takara
  • Wasu masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a karamar hukumar Sandamu ta jihar Katsina ne suka fara kokarin shigar da Yusuf Buhari siyasa
  • Wata majiya ta yi ikirarin cewa gwamnatin jihar Katsina na da ra'ayin goyon bayan takarar Yusuf Buhari, duk da ba ta fito ta yi bayani ba kai tsaye

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Sandamu ta jihar Katsina sun fara ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kan jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.

A wani shiri da suka yi, sun mara wa ɗan tsohon shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari, baya a matsayin ɗan takarar da suka fi so a mazaɓar Daura/Sandamu/Mai’adua.

Kara karanta wannan

INEC ta goge sunayen shugabannin ADC, tafiyar hadaka za ta iya rushewa

Dan tsohon shugaban kasa, Yusuf Buhari
Yusuf Buhari yayin wani taro a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa an cimma wannan matsaya ne a wani muhimmin taro da aka gudanar a sakatariyar ƙaramar hukumar Sandamu, wanda ya haɗa zaɓaɓɓun shugabanni da masu riƙe da muƙaman siyasa daga sassa daban-daban na mazaɓar.

Ana so Yusuf Buhari ya shiga takarar 2027

Da yake jawabi ga mahalarta taron, shugaban ƙaramar hukumar Sandamu, Usman Na Lado, ya bayyana cewa goyon bayan Yusuf matsaya ce ta bai ɗaya daga masu ruwa da tsaki, domin ƙarfafa damar jam’iyyar a zaɓe mai zuwa.

Rahotanni sun nuna cewa ya ce an zaɓi Yusuf Buhari ne bisa la’akari da ƙwarewarsa da kuma yadda yake da karɓuwa a cikin jam’iyyar a jihar Katsina.

Batun takarar Tinubu da Radda

Ya ƙara da cewa baya ga kujerar majalisar wakilai, taron ya kuma sake jaddada goyon baya ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dikko Umar Radda a matsayin ‘yan takarar shugaban ƙasa da gwamna na jam’iyyar a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Rundunar IRGC ta yi wa Isra'ila barna a sababbin hare haren makami mai linzami

Haka kuma, ya bayyana cewa masu ruwa da tsakin sun mara wa shugaban majalisar dokokin jihar Katsina, Nasiru Yahaya Daura, baya ya nemi kujerar Sanata Arewacin Katsina.

Lado ya ce wannan mataki na nuna fara shiri tun da wuri gabanin zaɓen 2027, tare da kira ga ‘yan jam’iyyar da su ƙara ƙoƙarin wayar da kan jama’a.

Matsayar Radda kan Yusuf Buhari

Wasu majiyoyi masu tushe a cikin jam’iyyar sun bayyana cewa goyon bayan da aka bai wa Yusuf Buhari ya fito ne kai tsaye daga gwamnan jihar.

Gwamna Dikko Umaru Radda
Gwamna Dikko Radda na jawabi a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Source: Facebook

Majiyar ta ce Yusuf Buhari shi ne ɗan takarar da gwamna Dikko Umaru Radda ya zaɓa domin tsayawa takara dan majalisar wakilai a zaben 2027.

'Yan majalisa na neman takara a APC

A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan majalisar wakilai da gwamnonin jam'iyyar APC sun fara neman tikitin takarar 2027 ba tare da zaben fitar da gwani ba.

Rahotanni sun nuna cewa wasu gwamnoni da wa'adin su zai kare sun fara shirin neman kujerun da 'yan majalisar ke rike da su a yanzuu.

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum sun fara kira ga APC da ta yi taka tsan-tsan wajen ba 'yan takara tikiti domin kaucewa rikici.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng