An Gano Matsalar da ADC za Ta Samu da INEC kan Takarar Shugaban Kasa
- Cif Femi Fani-Kayode ya bayyana halin ni 'ya su da jam'iyyar hamayya ta ADC za ta shiga gabanin babban zabe mai zuwa
- Kalamansa na zuwa ne bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta soke sunan David Mark daga matsayin Shugaban ADC
- Femi Fani-Kayode ya bayyana cewa tabbas, ADC na iya fuskantar matsala wajen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa da INEC za ta aminta da shi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jigo a APC, Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa jam’iyyar ADC na iya kasa fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa da hukumar INEC za ta amince da shi gabanin zaɓen 2027.
Ya bayyana haka ne awannai kadan da INEC ta sanar da soke sunan David Mark da wasu manyan jam'iyyar daga jagorancin ADC saboda hukuncin kotu.

Source: Twitter
Femi Fani Kayode ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba,1 ga watan Afrilu, 2026.
Fani Kayode ya hango wa ADC matsala
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Femi Fani Kayode ya soki halin da jam’iyyar adawa ke ciki na rikice-rikice da rashin jituwa.
A cewarsa, duk da ƙoƙarin da jam’iyyar ke yi na jawo manyan ‘yan siyasa da bayyana a kafafen yaɗa labarai, hakan ba zai wadatar ba idan har ba a warware matsalolin cikin gida ba.
Ya ce:
“Za su iya yin hayaniya yadda suke so, su jawo manyan mutane, su rika fitowa a talabijin suna tattaunawa marasa ma’ana, amma hakan ba zai canja gaskiyar da ke gabansu ba.”
Fani-Kayode ya ƙara da cewa rikice-rikicen cikin gida da bangarori masu gaba da juna na iya lalata damar da jam’iyyar ke da ita a zaɓe mai zuwa.
Fani Kayode ya gargadi jam'iyyar ADC

Kara karanta wannan
Bayan shigar Kwankwaso cikin jam'iyyar, ADC ta fallasa makarkashiyar da ake kulla mata
Tsohon ministan ya kuma gargadi ‘yan siyasa da ke tunanin shiga jam’iyyar ADC da su yi hattara, yana mai cewa hakan na iya zama aikin banza a ƙarshe. A cewarsa:
“Shiga ko goyon bayan ADC na iya zama ɓata lokaci ga duk wanda ya zaɓi bin wannan hanya mai cike da ƙalubale.”
Sai dai duk da sukar da ya yi, ya buƙaci jam’iyyar da ta gyara matsalolinta na cikin gida, ta daina kai juna kotu, tare da haɗa kai domin fitar da sahihin ɗan takara da INEC za ta amince da shi.

Source: Twitter
Ya ce:
“Ina kira gare su da su gyara gidansu, su birne bambance-bambance, su daina rikici a kotu domin su iya fitar da ɗan takara nagari da za mu fafata da shi a zaɓen 2027.”
Fani-Kayode ya kuma nuna kwarin gwiwa kan nasarar jam’iyyarsa ta APC a zaɓe mai zuwa, yana hasashen cewa za su samu gagarumar nasara a kan ‘yan adawa. Ya ce APC na da ƙarfin da za ta kayar da kowace jam’iyya, yana mai cewa ya kamata ‘yan adawa su shirya fuskantar babban ƙalubale a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
NNPP ta zama marigayiya: Kwankwasiyya ta faɗi yadda Kwankwaso zai raya ADC gabanin 2027
INEC ta sace gwiwar shugabannin ADC
A baya, mun wallafa cewa hukumar INEC karkashin shugabancin Farfesa Joash Amupitan ta rusa shugabannin jam'iyyar adawa ta ADC da David Mark ke jagoranta.
Hukumar zabe ta INEC ta fitar da sanarwar rusa shugabannin ne a ranar Laraba, 1 ga watan Maris, 2026, inda ta ce an riga an shigar da korafi a gaban kotu kan batun.
A shekarar da ta gabata ne manyan 'yan adawan Najeriya kamar Atiku Abubakar, Nasir El-Rufa'i da sauransu suka karbi ragamar ADC tare da David Mark a matsayin Shugaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
