APC na Shan Matsin Lamba kan Takarar 2027, an Yi Gargadin Rikici zai Barke

APC na Shan Matsin Lamba kan Takarar 2027, an Yi Gargadin Rikici zai Barke

  • Manyan jagororin jam'iyyar APC da suka hada da gwamnoni da 'yan majalisa na neman a ba su tikitin takara kai tsaye ba tare da zaben fitar da gwani ba
  • Masu jan ragamar APC sun nuna bukatar hakan ne yayin da 'yan siyasa da jam'iyyu suka fara shirye-shiryen siyasar 2027 da ta ke daukar hankali a yanzu
  • Wani mai sharhi kan lamuran siyasa, Mathew Ifeolu ya bayyana cewa bukatar gwamnoni da 'yan majalisun za ta iya haifar da babban rikici a APC

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC na fuskantar matsin lamba daga ‘yan majalisar tarayya da gwamnonin jihohi kan batun ba su tikitin tsayawa takara kai-tsaye gabanin zaɓen 2027.

Rahotanni sun nuna cewa sanatoci da ‘yan majalisar wakilai na neman tabbacin komawa kujerunsu, yayin da wasu gwamnonin jihohi masu shirin neman kujerar majalisar dattawa su ma ke neman tikitin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Zuwan Kwankwaso ADC ya tayar da magana, jam'iyyar ta 'gano' shirin APC

Yadda aka yi taron gwamnonin Arewa
Wasu gwamnonin Arewa yayin wani taro da suka yi. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Majiyoyin jam’iyyar sun shaidawa The Cable cewa har yanzu ba a yanke hukunci a hukumance ba, amma ana gudanar da tarurruka domin warware matsalar.

'Yan APC na neman tikitin takara

Shugabannin majalisar tarayya sun buƙaci a amince da tsarin tikitin kai-tsaye ga ‘yan majalisa masu ci, suna cewa hakan na da muhimmanci wajen ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke yi.

An ce an gabatar da wannan buƙatar ne a babban taron jam’iyyar APC na kasa da aka gudanar a Eagle Square da ke Abuja.

Da yake magana a madadin ‘yan APC, Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce bai wa ‘yan majalisa masu aiki tukuru na da muhimmanci.

Abbas Tajudeen a taron APC
Shugaban majalisar wakilai a taron APC a Abuja. Hoto: Abbas Tajudeen
Source: Facebook

Ya ce hakan zai ba su damar komawa kai-tsaye zai taimaka wajen tabbatar da daidaito, kwanciyar hankali, da aiwatar da manufofi a ƙarƙashin ajandar “Renewed Hope”.

Tsoron da 'yan jam'iyyar APC ke yi

Kara karanta wannan

Watakila ADC ta gyara zama a Sokoto, Sanatan APC na tunanin sauya sheka

Duk da haka, wasu ‘yan majalisa na nuna damuwa kan yunƙurin wasu gwamnoni na hana su komawa majalisa. An rahoto cewa wasu gwamnoni na ƙoƙarin sauya wasu ‘yan majalisa ko kuma su kansu su nemi kujerun.

Wata ta ce wannan rikici ya saɓa da wani tsarin da ake cewa gwamnoni ne za su fitar da ‘yan takarar majalisar jihohi, yayin da shugaban ƙasa zai yanke hukunci kan ‘yan takarar majalisa.

Abin da zai iya tarwatsa APC a 2027

Masana siyasa, ciki har da Mathew Ifeolu, sun yi gargadin cewa idan ba a kula da wannan batu da kyau ba, zai iya jawo rikici mai tsanani a cikin jam’iyyar APC.

A wata hira da Daily Trust, ya ce yawancin rikice-rikicen siyasa kan taso ne bayan zaɓen fitar da gwani, don haka ya shawarci shugabannin APC su tafiyar da lamarin cikin gaskiya da adalci.

Abdullahi Ganduje ya gana da Shugaba Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da tsohon Shuugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Bayan ganawar, Abdullahi Ganduje ya fitar da sanarwar cewa sun tattauna wasu lamuran da suka shafi siyasa tare da shugaban kasar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso da Nasiru Yusuf Gawuna suka koma jam'iyyar ADC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng