"Mun San Kwankwaso ba Kanwar Lasa ba ne": Jagora a APC Ya Ce Suna Shirin Karo da Madugu

"Mun San Kwankwaso ba Kanwar Lasa ba ne": Jagora a APC Ya Ce Suna Shirin Karo da Madugu

  • Jigon APC, Hon. Adamu Aliyu, ya ce ba za a iya yin watsi da tasirin jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso a Kano ba
  • Ya bayyana cewa APC na ƙoƙarin fuskantar tasirin Kwankwaso ba tare da raina shi ba yayin da ake shirin zabe mai zuwa
  • Ya yi kira ga ‘yan Arewa da ke fushi su dawo su mara wa jam’iyyar baya domin APC ce hanyar bullewa a 2027

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Wani jigo a jam’iyyar APC, Hon. Adamu Aliyu, ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da suke yi na ƙarfafa jam’iyyarsu, ba za su iya yin watsi da tasirin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a siyasar Kano ba.

Aliyu ya ce jam’iyyarsa na sane da irin ƙarfin da Kwankwaso yake da shi, musamman a jihar Kano, inda ya dade yana da magoya baya masu yawa.

Kara karanta wannan

"Tinubu ya dimauce da Kwankwaso ya koma ADC": 'Dan Takarar Gwamna a 2023

Jigo a APC ya sara wa Kwankwaso
Shugaban APC Yilwatda, Dandazon magoya baya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: @officialAPCng/Rabiu kwnakwaso
Source: Twitter

A hira da ya yi da Channels TV, ya jaddada cewa APC ba za ta zauna kawai tana kallo ba, amma tana ɗaukar matakan da suka dace domin fuskantar wannan ƙarfi.

APC na shiri a kan Kwankwaso

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Hon. Adamu Aliyu ya bayyana cewa duk da APC na jinjina ƙarfi da tasirin Kwankwaso, wannan ba ya nufin ana tsoronsa a siyasar Najeriya.

A cewarsa:

“Babu wanda zai iya yin watsi da Kwankwaso a Kano, kuma mu ba mu yi watsi da tasirinsa ba. Mun san abin da zai iya yi, kuma muna ƙoƙarin dakile shi.”

Ya ƙara da cewa jam’iyyarsu na girmama Kwankwaso da kuma mabiyansa, amma hakan ba yana nufin za su yi sakaci.

A kalamansa:

“Muna girmama shi da magoya bayansa, amma mu ma muna nan. Za mu yi duk mai yiwuwa don kula da abin da ke faruwa da kuma yadda za mu tunkare shi."

Kara karanta wannan

'Mun rasa Kano': Jigon jam'iyyar APC ya cire rai bayan Kwankwaso ya koma ADC

APC ta shirya wa Kwankwaso

Hon. Adamu Aliyu ya bayyana cewa APC na da cikakken shiri da dabaru da za su taimaka wajen rage tasirin Kwankwaso a siyasar Kano, yana mai cewa suna sane da yadda yake tafiyar da harkokinsa.

A wani ɓangare, jigon na APC ya yi kira ga ‘yan Arewa da suka nuna rashin jin daɗi da wasu lamura a jam’iyyar da su sake tunani su dawo cikin APC domin haɗa kai.

APC ta ce tana shiri don rage tasirin
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a tsakiyar magoya bayansa Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Ya ce:

“Muna roƙon ‘yan uwa daga Arewa da ke jin haushi su dawo, su shiga cikin wannan gwamnati. Domin ko ana so ko ba a so, alamu sun nuna APC ce za ta lashe zaɓe.”

Haka kuma, ya jaddada cewa jam’iyyar za ta yi duk abin da doka ta tanada domin ganin ɗan takararta ya zama shugaban ƙasa.

Dangane da batun sauyin siyasa a Kano, Hon. Adamu Aliyu ya ce akwai manyan ‘yan siyasa da suka sauya sheƙa zuwa APC daga ɓangaren Kwankwaso, daga ciki har da wasu magoya bayansa.

Kara karanta wannan

NNPP ta zama marigayiya: Kwankwasiyya ta faɗi yadda Kwankwaso zai raya ADC gabanin 2027

Kwankwaso ya rikita APC – Yakasai

A baya, mun wallafa cewa tsohon hadimin Shugaban APC na kasa, Salihu Tanko Yakasai ya ce sauya shekar Rabiu Kwankwaso ADC ta rikita jam'iyya mai-ci.

Dawisu ya bayyana cewa idan aka lura da kyau, tun bayan da Kwankwaso a yanki tikitin zama dan ADC, manyan APC suka kasa zama irin wanda ba a yi a baya.

Ya yi zargin cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na nuna alamun fargaba kan sabon hadakar siyasa da jiga-jigan 'yan adawa suka dauko a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng