Bayan Shigar Kwankwaso cikin Jam'iyyar, ADC Ta Fallasa Makarkashiyar da Ake Kulla Mata
- Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta fito ta yi wasu zarge-zarge kan gwamnatin APC mai mulki a kasar nan
- Sakataren yada labarai na ADC ya bayyana akwai shirin da ake kullawa biyo bayan sauya shekar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar
- Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa ana son matsawa hukumar INEC lamba domin ta yi wani abu kan shugabancin jam'iyyar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam'iyyar ADC ta yi zargin cewa ana shirya mata wata sabuwar makarkashiya.
ADC ta zargi wasu wakilan gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki da shirya wata zanga-zanga a Abuja da nufin dagula lissafin jam’iyyar adawar.

Source: Facebook
Sakataren yaɗa labarai na ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Laraba, 1 ga watan Maris 2026.
Wane zargi jam'iyyar ADC ta yi?

Kara karanta wannan
An buga kugen siyasa; Kwankwaso ya sa labule da Atiku, an ji abin da suka tattauna
Bolaji Abdullahi ya ce wannan zargin maƙarƙashiya ya biyo bayan ficewar Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano, daga tsohuwar jam'iyyarsa zuwa ADC.
“A jiya, mun fallasa wata muguwar maƙarƙashiya da wasu wakilan gwamnatin APC mai mulki suka ƙulla na matsa wa INEC lamba don ɗaukar matakin da ya saɓa wa doka domin dagula jam’iyyarmu, biyo bayan gagarumin sauyin sheka na Rabiu Kwankwaso zuwa ADC."
- Bolaji Abdullahi
ADC ta ce ana matsawa INEC lamba
Ya yi iƙirarin cewa yunƙurin matsa wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta lasa (INEC) lamba ya fuskanci cikas.
“Bayan sun gamu da cikas a wajen INEC, yanzu sun sauya salon takunsu, amma manufarsu tana nan guda ɗaya."
- Bolaji Abdullahi
A cewarsa, bayanan da jam’iyyar ke da su sun nuna cewa ana shirin gudanar da zanga-zanga a Abuja.
“Bayanai da suke iske mu a safiyar yau sun nuna cewa ana shirin gudanar da zanga-zanga a gobe Alhamis, 2 ga Afrilu, a Abuja, wadda wani sanannen minista yake ɗaukar nauyinta."
- Bolaji Abdullahi
Wane shiri aka kulla kan ADC?
Bolaji Abdullahi ya yi zargin cewa waɗanda ke goyon bayan zanga-zangar suna da niyyar tattaro mutanen da za su yi basaja a matsayin mambobin ADC.
“Shirin abu ne mai sauƙi, tattaro mutanen da aka biya kuɗi, suna nuna kansu a matsayin mambobin jam’iyyar da ba a yi wa adalci ba, za su fito kan tituna suna neman ‘Dole David Mark ya yi murabus'."
- Bolaji Abdullahi

Source: Twitter
Ya ƙara da cewa manufar zanga-zangar ita ce matsa wa INEC lamba don ta amince da wani jagoran daban a cikin jam’iyyar.
“Suna fatan hakan zai haifar da ‘matsin lamba daga jama'a’ ga shugaban INEC domin ya ɗaukaka tare da amincewa da wani mutum wanda ya yi murabus daga muƙaminsa kuma aka kore shi daga ADC, zuwa matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa, alhali ba ma ɗan jam’iyyar ba ne."
- Bolaji Abdullahi
Kakakin na ADC ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da mayar da hankali kan ayyukanta tare da nuna juriya ga abin da ta bayyana a matsayin yunƙurin tsoma baki a cikin harkokinta.
Nasiru Gawuna ya koma jam'iyyar ADC

Kara karanta wannan
NNPP ta zama marigayiya: Kwankwasiyya ta faɗi yadda Kwankwaso zai raya ADC gabanin 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar Gwamnan jihar Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC.
Tsohon mataimakin gwamnan ya kammala rajista tare da karɓar katin zama mamba na jam'iyyar a ranar Talata, 31 ga watan Maris 2026.
Gawuna ya bayyana cewa a karan kansa ne ya yanke shawarar ficewarsa daga jam'iyyar APC, wadda ya taba yin takarar gwamna a karkashinta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
