"Tinubu Ya Dimauce da Kwankwaso Ya Koma ADC": 'Dan Takarar Gwamna a 2023

"Tinubu Ya Dimauce da Kwankwaso Ya Koma ADC": 'Dan Takarar Gwamna a 2023

  • Tsohon hadimin Shugaban APC na kasa, Salihu Tanko Yakasai ya ce sauya shekar Rabiu Kwankwaso ADC ta rikita jam'iyya mai-ci
  • Dawisu ya bayyana cewa idan aka lura da kyau, tun bayan da Kwankwaso a yanki tikitin zama dan ADC, manyan APC suka kasa zama
  • Ya yi zargin cewa Shugaba Tinubu na nuna alamun fargaba kan sabon hadakar siyasa da jiga-jigan 'yan adawa suka dauko a kasar nan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon hadimin Shugaban APC na kasa, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa sauya shekar Rabiu Musa Kwankwaso ta rikita APC.

A farkon makon nan ne jagoran Kwankwasiyya na kasa, Kwankwaso ya tara dubunnan masoya a Kano inda ya karbi shahadar shiga ADC.

Kara karanta wannan

"Ba Legas ba ce"; Tsohon 'dan takarar gwamna ya fadi abin da Tinubu ba zai iya a Kano ba

Salihu Tanko Yakasai ya ce an ruda Tinubu
Salihu Tanko Yakasai daga hagu, Shugaban kasa Bola Tinubu daga dama Hoto: Salihu Tanko Yakasai/Bayo Onanuga
Source: Twitter

A hira da ya yi da Trust TV, Yakasai ya bayyana cewa shigar Kwankwaso ADC ya riga ya sauya akalar siyasa a jihar Kano, ba wai zai sauya ba nan gaba.

Kwankwaso ya canja siyasar Kano - Yakasai

Yakasai ya bayyana cewa akwai abubuwa da dama da suka tabbatar da cewa siyasar Kano ta canja kuma an girgiza APC daga kasa har sama.

A cewarsa:

“Ba wai zai sauya ba ne, ya riga ya sauya komaI."

Yakasai ya kawo misalai uku domin nuna yadda lamarin ya fara tasiri kai tsaye. Ya ce bayan wani taro da aka yi, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gana da tsofaffin ‘yan majalisar wakilai na jam’iyyar APC.

Haka kuma, ya kara da cewa gwamnan ya sake ganawa da ‘yan majalisar wakilai masu ci da kuma sanatoci, duk da cewa ba dukkansu suka halarta ba.

Ya bayyana cewa wannan jerin ganawa ya nuna yadda ake kokarin daidaita al’amura cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

'Mun rasa Kano': Jigon jam'iyyar APC ya cire rai bayan Kwankwaso ya koma ADC

Yakasai: "An warware rikici a APC"

Game da Kawu Sumaila, Salihu Tanko Yakasai ya ce Sanatan ya gana da gwamnan, inda aka warware wasu matsaloli da ke tsakaninsu.

Ana ganin Kwankwaso ya gigita Tinubu
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Bola Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

A cewarsa, wadannan matakai sun nuna cewa akwai sauyi mai girma da ya fara faruwa a fagen siyasar Kano.

Salihu Tanko Yakasai ya kuma yi zargin cewa ba Kano kadai ba ce ke fuskantar wannan sauyi, har ma da matakin kasa baki daya.

Ya ce:

“Ba jiha kadai ba ce ke cikin fargaba, har da kasa baki daya, har da shugaban kasa kansa.”

Ya bayyana cewa ya ga rahotannin ganawar tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da wasu gwamnoni, yana mai cewa wannan na nuna akwai damuwa.

A cewarsa, irin wannan ganawa ta musamman tsakanin shugaban kasa da Ganduje ba ta saba faruwa ba tun bayan murabus din Ganduje daga shugabancin jam’iyyar APC.

Yakasai ya ce faruwar wadannan ganawa jim kadan bayan sauyin Kwankwaso da wasu jiga-jigan siyasa zuwa ADC na nuna cewa ana kokarin shawo kan matsalar da suka shiga.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya jawo wa ADC canji mai girma awanni kadan bayan ya sauya sheka

An gano wani shirin Tinubu kan ADC

A wani labarin, mun wallafa cewa tsohon dan takarar gwamna jihar Kano a zaben 2023, Salihu Tanko Yakasai, ya yi magana kan wani shiri na Shugaba Bola Tinubu.

Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi kuskuren tunanin mayar Kano jiha dake karkashin jam'iyya daya, lamarin da a yanzu an aka ba shi mamaki.

Tsohon dan takarar gwamnan ya nuna cewa akwai bambanci tsakanin jihar Kano da Legas, kuma jama'a za su tabbatar da hakan musamman a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng