"Ba Legas ba ce"; Tsohon 'Dan Takarar Gwamna Ya Fadi Abin da Tinubu ba Zai Iya a Kano ba

"Ba Legas ba ce"; Tsohon 'Dan Takarar Gwamna Ya Fadi Abin da Tinubu ba Zai Iya a Kano ba

  • Tsohon dan takarar gwamna jihar Kano a zaben 2023, Salihu Tanko Yakasai, ya yi magana kan wani shiri na Shugaba Bola Tinubu
  • Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi kuskuren tunanin mayar Kano jiha dake karkashin jam'iyya daya
  • Tsohon dan takarar gwamnan ya nuna cewa akwai bambanci tsakanin jihar Kano da Legas, kuma jama'a za su tabbatar da hakan

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PRP a Kano a zaɓen 2023, Salihu Tanko Yakasai, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da karfa-karfa.

Salihu Tanko Yakasai ya ce Tinubu na kokarin mayar da jihar Kano jiha da ke karkashin jam’iyya ɗaya, inda ya bayyana hakan a matsayin babban kuskuren lissafi.

Dawisu ya ce Tinubu na son mayar da Kano jam'iyya daya
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Salihu Tanko Yakasai Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Source: Facebook

Salihu Tanko Yakasai ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 1 ga watan Afrilun 2026.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Gawuna ya shiga sabuwar jam'iyya don karawa da Abba a 2027

Salihu Yakasai ya fadi kuskuren Bola Tinubu

Ya bayyana cewa Tinubu ya yi kuskuren fahimtar siyasar Kano, inda har yake tunanin mayar da jihar karkashin jam'iyya daya ba tare da bin hanyar kawo ci gaba ba.

"Shugaba Bola Tinubu na tunanin zai iya mayar da Kano jiha mai jam’iyya daya, ba ta hanyar ayyukan cigaba da inganta rayuwar al’umma ba, sai ta hanyar dabarun siyasa? Wannan fahimtar ta sa kuskure ce akan siyasar Kano."
"Tun daga zamanin NEPU har zuwa lokacin Santsi da Tabo, Kano ba ta taba zama jiha mai jam’iyya daya ba, kuma ba za ta taba zama haka ba. Kano ba Legas ba ce!"

- Salihu Tanko Yakasai

Wace irin adawa Kano ke yi?

A cewarsa, adawa a Kano ba ana yin ta ba ne kawai don adawa, amma ana yin ta ne don tabbatar da ci gaban al’umma, kyakkyawan shugabanci, adalci, da kuma riƙon amana.

"Kano jiha ce ta siyasar kishin al’umma da tsayawa kan gaskiya, tarbiyar da Mallam Aminu Kano yai mana kenan."

Kara karanta wannan

2027: Minista na 3 ya mika wa Tinubu takardar murabus, zai tsaya takarar gwamna

"Ba mu adawa don kawai mu yi adawa; muna adawa ne domin neman ci gaban kasa da al'umma, ingantaccen shugabanci, adalci da rikon amana."

- Salihu Tanko Yakasai

Salihu Tanko Yakasai ya yi magana kan Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Yakasai ya ce an yi watsi da Kano

Haka zalika, Yakasai ya nuna damuwarsa kan abin da ya kira watsi da korafe-korafen mutanen jihar Kano, musamman zargin son zuciya wajen naɗe-naɗen gwamnati da kuma ba wa wasu yankuna fifiko a ayyukan ci gaba.

"Me aka yi wa Kano da zai sa Tinubu yai tunanin kowa sai ya goyi bayan sa? Lokacin da muke ta kokawa akan yadda aka mayar da hankali kan ayyuka a Legas da kuma yadda aka karkatar da nade-naden mukamai ga yarbawa kadai, an yi watsi da wadannan korafe-korafen, hasali ma yan'uwansa yarbawa bin mu sukai da zagi da cin mutunci."

- Salihu Tanko Yakasai

Ya jaddada cewa ana samun biyayya ga shugabanci ne ta hanyar adalci da kyakkyawan mulki, ba ta hanyar tursasawa, makircin siyasa, ko yaudara ba.

Wane gargadi Yakasai ya yi?

A ƙarshe, ya yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da hana Kano haƙƙinta na ci gaba, mutanen jihar za su mayar da martani ta hanyar akwatin zaɓe a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Mojtaba Khamenei: Daga karshe an bayyana kasar da sabon jagoran addini na Iran yake

"Biyayya ga shugabanci na samuwa ne ta hanyar adalci da kyautatawa, ba a tilasta shi ta dabarun siyasa da wayo ko cin amana."
"Tunda aka hana Kano cigaba, toh Kano za ta mayar da martani a akwatin zabe. Wannan shi ya fi komai sauki!"
"Falle daya ce (F1)."

- Salihu Tanko Yakasai

Ganduje ya gana da Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ganduje ya gana da Shugaba Tinubu ne biyo bayan sauya shekar tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, zuwa jam'iyyar ADC.

Tsohon gwamnan ya ce sun tattauna muhimman batutuwan ƙasa, harkokin jam’iyya, da kuma matakan da za su taimaka wajen ci gaban jihar Kano da ma Najeriya baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng