Ganduje Ya Fadi Me Ya Tattauna da Tinubu bayan Sauya Shekar Kwankwaso, Gawuna

Ganduje Ya Fadi Me Ya Tattauna da Tinubu bayan Sauya Shekar Kwankwaso, Gawuna

  • Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana bayan ganawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock Villa
  • A daya bangare kuma, shugaba Bola Tinubu ya tattauna da tsohon ministan tsaron Najeriya kuma tsohon gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar
  • Hakan na zuwa bayan yanayin siyasar jihar Kano ya fara samun gagarumin sauyin da ya shafi APC, inda Nasir Yusuf Gawuna ya koma ADC

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, da tsohon ministan tsaro, Badaru Abubakar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Ganawar ta zo ne kwana guda bayan tsohon gwamnan Kano kuma jigo a jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC tare da Yusuf Gawuna.

Kara karanta wannan

2027: Minista na 3 ya mika wa Tinubu takardar murabus, zai tsaya takarar gwamna

Bola Tinubu da Abdullahi Umar Ganduje
Shugaba Bola Tinubu na gaisawa da Abdullahi Ganduje. Hoto: @GovUmarGandujee
Source: Twitter

Legit Hausa ta tattaro wasu bayanai da Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi a shafinsa na X bayan ganawa da shugaban kasa a Abuja.

Ganduje ya gana da Tinubu a Abuja

An hango Ganduje, sanye da koriyar babbar riga, yana fita daga fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 4:15 na yamma, yayin da Badaru ya fice kusan mintuna 15 bayan haka da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

Dukkaninsu sun ƙi yin magana da ‘yan jarida kan dalilin ziyarar tasu, sai dai Ganduje ya fitar da sanarwa kan abubuwa da suka tattauna da Tinubu, inda ya ce:

“A yau (Talata) na samu damar ganawa da mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja.
Mun tattauna muhimman batutuwan ƙasa, harkokin jam’iyya, da kuma matakan da za su taimaka wajen ci gaban jiharmu da ma Najeriya baki ɗaya.”

Matsayin Ganduje a jam'iyyar APC

Kara karanta wannan

Watakila ADC ta gyara zama a Sokoto, Sanatan APC na tunanin sauya sheka

Ganduje ya rike mukamin shugaban APC na ƙasa daga watan Agusta 2023 zuwa Yulin 2025, inda ya yi murabus daga mukamin saboda dalilan rashin lafiya.

Daga baya, Farfesa Nentawe Yilwatda ya gaje shi bayan an zaɓe shi a matsayin cikakken shugaban jam’iyyar a babban taron zaɓen shugabanni na jam’iyyar karo na huɗu da aka gudanar a ranar 27 ga Maris, 2026.

Kafin zama shugaban jam'iyyar, Ganduje ya kasance gwamnan Kano daga 2015 zuwa 2023 kuma a yanzu yana daga cikin manyan jagororin APC a jihar.

Matsayin Badaru a Najeriya

Shi kuma Badaru, tsohon gwamnan jihar Jigawa daga 2015 zuwa 2023, ya yi aiki a matsayin M8inistan tsaro a gwamnatin Tinubu kafin murabus dinsa na baya-bayan nan.

Punch ta wallafa cewa fita daban-daban da suka yi daga fadar sun nuna cewa ganawar tasu ta kasance daban-daban, ba tare da zama na haɗin gwiwa da shugaban ƙasar ba.

Badaru Abubakar kafin murabus
Badaru Abubakar a lokacin da ya ke Ministan tsaro. Hoto: Mati Ali
Source: Facebook

Ana ganin ziyarar na iya kasancewa tana da alaƙa da sake tsara jam’iyyar bayan babban taron APC na ƙasa da kuma yawaitar sauya sheƙa da ake gani a jihohin Kano da Jigawa.

Kara karanta wannan

Bayan watsi da taron Abba, Sanata Kawu Sumaila ya sa labule da manyan APC

Tsohon minista ya fita daga APC

A wani labarin, kun ji cewa tsohon ministan shari'a a Najeriya, Michael Aondoakaa ya sanar da fita daga jam'iyyar APC mai mulki.

Michael Aondoakaa ya bayyana cewa ya fita daga APC ne domin mayar da hankali kan wasu muhimman abubuwa a jihar Benue.

Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan kokarin da ya yi wa jiharsa tare da cewa ya gode bisa damar da aka ba shi wajen gina APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng