2027: Minista na 3 Ya Mika wa Tinubu Takardar Murabus, Zai Tsaya Takarar Gwamna
- Ministan sufuri, Sa’idu Alkali ya mika takardar murabus dinsa ga Shugaba Bola Tinubu a yau Talata, inda ake zargin zai tsaya takarar gwamna
- Murabus din yana karkashin umarnin da shugaban kasa ya bayar cewa dukkan masu rike da mukaman siyasa su sauka kafin karshen Maris
- Sa’idu Alkali ya bi sahu Yusuf Tuggar da Yusuf Sununu wadanda suma suka yi murabus domin neman wasu kujerun a zaben shekarar 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Sanata Sa’idu Alkali, ya yi murabus daga muƙaminsa na ministan sufurin Najeriya, wanda ya kawo karshen zamansa a majalisar zartarwar Shugaba Bola Tinubu a yau Talata.
Fadar shugaban ƙasa ce ta bayyana hakan, inda ta nuna cewa ministan ya ɗauki wannan mataki ne sa'o'i kaɗan kafin cikar wa'adin ranar 31 ga Maris, 2026 da shugaban ƙasar ya gindaya.

Source: Facebook
Ministan sufuri ya yi murabus daga mukaminsa
Sanata Alkali, wanda ɗan asalin jihar Gombe ne, ya sanar da murabus din nasa ne bayan ya gana da Shugaba Tinubu a fadar shugaban ƙasa dake Abuja, in ji rahoton The Cable.
Ana sa ran tsohon ministan zai tsaya takarar kujerar gwamnan jihar Gombe a babban zaɓen 2027 dake tafe domin maye gurbin Gwamna Inuwa Yahaya.
Gwamna Inuwa Yahaya dai, wanda aka zaɓa a 2019, aka sake zaɓarsa a 2023 ƙarƙashin jam'iyyar APC, zai kammala wa'adin mulkinsa na biyu a watan Mayun 2027.
Bin dokar zaɓe ta shekarar 2026
Wannan murabus ya biyo bayan umarnin da Shugaba Tinubu ya bayar ta hannun sakataren gwamnatin tarayya a ranar 17 ga Maris, 2026, dake neman dukkan masu neman takara su ajiye aiki.
Wasiƙar wadda Sanata George Akume ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa wannan mataki yana bin sashe na 88(1) na dokar zaɓe ta shekarar 2026 domin samar da adalci ga kowa, kamar yadda muka ruwaito.
Dokar dai ta buƙaci ,inistoci, masu ba da shawara, da shugabannin hukumomi su yi murabus kafin su shiga zaɓen fitar da gwani na jam'iyyunsu domin kada su yi amfani da ofishinsu don samun tagomashi.
Ministocin da suka yi murabus zuwa yanzu
Sanata Sa’idu Alkali shi ne minista na uku da ya yi murabus a cikin kwanaki biyu domin bin umarnin shugaban ƙasa da kuma dokokin hukumar zaɓe (INEC), a cewar rahoton Punch.

Source: Facebook
A jiya Litinin, mun ruwaito cewa ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, da karamin ministan jin-ƙai, Dr. Yusuf Sununu, sun yi murabus domin takarar gwamnan Bauchi da kuma kujerar sanata a jihar Kebbi.
Hukumar INEC ta riga ta tsara gudanar da zaɓen fitar da gwani tsakanin 23 ga Afrilu zuwa 30 ga Mayu, 2026, wanda hakan ya sa ƴan siyasa ke gaggawar mika takardun murabus dinsu.
Kafin naɗa shi matsayin minista, Sa’idu Alkali ya wakilci mazaɓar Gombe ta Tsakiya a majalisar dattawa, inda yanzu yake shirin komawa fagen siyasar jiharsa gadan-gadan.
Asali: Legit.ng

