Bayan Shiga ADC, Kwankwaso Ya Aika Sako ga 'Yan Najeriya kan Zaben 2027
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi muhimmin kira ga 'yan Najeriya kan zaben shekarar 2027 da ake tunkara
- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa zaben 2027 yana da muhimmanci matuka saboda haka bai kamata a yi wasa da shi ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya buƙaci ’yan Najeriya da su ba babban zaɓen shekarar 2027 fifiko da muhimmanci matuƙa.
Sanata Kwankwaso ya jaddada buƙatar shiga harkokin siyasa da yin rajistar zaɓe.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi lokacin karbar katin zama ɗan jam’iyyar ADC a Kano.
Kwankwaso ya shiga ADC
Tsohon gwamnan na jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya koma ADC ne a hukumance a yau Litinin, 30 ga watan Maris 2026.
Kwankwaso ya yi rajista a matsayin ɗan jam’iyya kuma ya karɓi katinsa na jam’iyya a ranar Litinin a Gidan Kwankwasiyya da ke Miller Road, Bompai, Kano.
Wane kira Kwankwaso ya yi ga 'yan Najeriya?
Kwankwaso ya yi kira ga magoya bayansa da su mallaki katin zama jam’iyyar ADC da kuma katin zaɓe na INEC, inda ya bayyana su a matsayin abubuwan muhimmanci wajen amfani da haƙƙinsu na dimokuraɗiyya, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.
“Babban zaɓen 2027 na musamman ne. Dole ne mu ba shi dukkan muhimmancin da ya dace."
“Daga yanzu, kafin ka samu damar shiga gidana, dole ne ka nuna katin zama ɗan jam’iyyar ADC da katin zaɓe na INEC a matsayin izinin shiga."
"Saboda haka, ina kira gare ku da ku je ku tabbatar kun yi rajista da ADC kuma kun karɓi katin zaɓenku.”
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Kwankwaso ya tara taro
Taron ya samu halartar manyan jiga-jigai, waɗanda suka haɗa da shugaban jam’iyyar ADC na kasa, Sanata David Mark, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023 Peter Obi, tsohon shugaban APC na kasa, John Odigie-Oyegun, da kuma Aminu Tambuwal.
Sauran manyan baƙi da suka halarta sun haɗa da tsohon Ministan cikin gida Rauf Aregbesola tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilai Emeka Ihedioha, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal.

Source: Facebook
Hakazalika, tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina Dr. Mustapha Muhammad, Kashim Ibrahim Imam, da Lawal Daura, da sauransu sun halarci taron.
Saƙon na Kwankwaso ya fito da muhimmancin shiga harkokin siyasa da haɗin kai yayin da Najeriya ke fuskantar zaɓen 2027, wanda ke nuna sabon yunkuri na tattara ’yan adawa gabanin zaɓen.
Kwankwaso ya yi murabus daga NNPP
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi murabus daga jam'iyyar NNPP.
Jagoran siyasar Kwankwasiyya ya bayyana cewa yana bukatar sake daidaita tafiyar siyasarsa domin nasara a zaben 2027.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne bisa la’akari da yadda siyasar Najeriya ke tafiya a yanzu, wanda ke bukatar sabon tsari mai inganci.
Asali: Legit.ng

