Atiku Ya Yi Murabus daga Harkokin Siyasa? Gaskiyar Zance Ta Fito
- An yada wasu rahotanni masu cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya hakura da harkokin siyasa
- Atiku Abubakar ya fito ya yi martani kan wadannan rahotannin masu ikirarin cewa ya koma gefe tare da yin murabus daga siyasa
- Tsohon mataimakin shugaban kasar na Najeriya ya yi zargi kan wadanda ke yada irin wadannan labaran a kansa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa ya daina siyasa.
Atiku Abubakar ya musanta rahotannin da ke yawo masu cewa ya yanke shawarar daina harkokin siyasa gadan-gadan.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran Atiku ya fitar, wadda hadiminsa Paul Ibe, ya sanya a shafinsa na X a ranar Litinin, 30 ga watan Maris 2026.
Atiku Abubakar ya musanta batun daina siyasa
Yayin da yake bayyana wannan jita-jita a matsayin labarin ƙarya, jigon na jam’iyyar ADC zargi gwamnatin tarayya da kasancewa bayan wannan rahoton.
Atiku ya nuna cewa rahoton da ya kira "ƙarya" yana ɗauke da dukkan alamun "shiryayyen yaƙin yaɗa labaran ƙarya da aka tsara don haifar da ruɗani, raunana karsashi, da kuma yaudarar al'ummar Najeriya."
Sanarwar ta ce:
"Muna son bayyanawa a hukumance cewa, bayanan da ke yawo a shafukan sada zumunta game da zargin wata ganawa da Atiku Abubakar ya yi da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ADC."
"Inda aka yi iƙirarin cewa tsohon Mataimakin shugaban kasar ya yanke shawarar 'komawa gefe tare da yin murabus daga harkokin siyasa,' ƙarya ce tsagwaronta kuma an yi ta ne da gangan don yaudara."
"Wazirin Adamawa bai gudanar da wata ganawa makamanciyar wannan da masu ruwa da tsaki na ADC a matakin ƙasa ba a 'yan kwanakin nan. Ganawa guda ɗaya tilo da ya yi kwanan nan ita ce da masu ruwa da tsaki na ADC na jihar Adamawa a ranar Alhamis ɗin da ta gabata."
Atiku zai sanar idan ya shirya barin siyasa
Ofishin yaɗa labarai na Atiku ya bayyana cewa, batu mai muhimmanci da tasiri kamar daina harkokin siyasa ba zai taɓa kasancewa ta hanyar jita-jita ba.
Sun bayyana cewa irin wannan shawara, idan har an yanke ta, za a sanar da ita ne a hukumance ta hanyar ofishin yaɗa labarai na Atiku.
Jagoran adawa ya nuna yatsa ga gwamnati
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
"Wannan sabuwar ƙarya tana ɗauke da dukkan alamun shiryayyen yaƙin yaɗa labaran ƙarya da aka tsara don haifar da ruɗani, raunana karsashi, da kuma yaudarar al'ummar Najeriya."
"Gwamnati da ma'aikatanta ne kawai za su iya ɗaukar nauyin wannan ƙage na yanke ƙauna saboda tsoron abin da ke tafe."
"Muna bayyanawa ba tare da wata shakka ba cewa, wannan makirci wasu abubuwa ne masu adawa da demokraɗiyya ke tura shi, waɗanda suka firgita ƙwarai da yadda ake samun haɗin kan ƙasa don ceto Najeriya daga gazawar gwamnatin yanzu."
"Saboda haka, muna kira ga magoya bayan Atiku Abubakar, mambobin ADC, da dukkan 'yan Najeriya masu kishin ƙasa da su yi watsi da wannan labarin ƙarya gaba ɗayansa, kuma su ci gaba da mayar da hankali kan ƙoƙarin haɗin gwiwa na ƙwato tare da sake gina ƙasarmu."

Source: Twitter
Gwamna Sule ya musanta ganawa da Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Abdullahi Sule na jihar Adamawa, ya yi martani kan rahotannin da ke cewa ya gana da Atiku Abubakar a Saudiyya.
Gwamna Abdullahi Sule ya musanta rahotannin da ke zargin cewa ya gudanar da wata ganawar sirri da Atiku Abubakar a birnin Makka na ƙasar Saudiyya.
Hakazalika, Gwamna Sule ya bayyana cewa bai yi wata ganawa da Atiku ko na kusa da shi ba yayin gudanar da Umrah a kasa mai tsarki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


