Kwankwaso na Shirin Sauya Sheƙa, ADC Ta Fadi yadda Za Ta Zaɓi Ƴan Takararta a 2027
- Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa tana kokarin daukar tsarin maslaha wajen zabar dan takarar shugaban kasa na 2027 domin rage kashe kudi da rikice-rikice
- Kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya ce suna da zabin zaben kai tsaye ko maslaha, amma sun cire zaben wakilai bisa dokar zabe da aka gyara
- Abdullahi ya soki APC yana cewa karfin jam’iyyar yana hannun shugabanta, kuma idan Bola Tinubu ya bar mulki jam’iyyar za ta ruguje cikin sauri
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Jam’iyyar adawa ta ADC ta yi magana game da yadda za ta fitar da dan takarar shugaban kasa.
Jam'iyyar ta bayyana cewa tana kokarin daukar tsarin maslaha wajen zabar dan takarar shugaban kasa a zaben 2027 mai zuwa a Najeriya.

Source: Facebook
Bolaji Abdullahi, kakakin yada labarai na kasa na jam’iyyar, ya bayyana haka yayin wata hira da aka yi da shi a shirin talabijin na Arise.
2027: Yadda ADC za ta zabi dan takara
Ya ce jam’iyyar na da zabin gudanar da zaben kai tsaye ko kuma tsarin maslaha wajen fitar da dan takara, amma an cire tsarin zaben wakilai.
Ya kara da cewa an cire zaben wakilai ne saboda dokar zabe da aka yi wa gyara, wadda ba ta goyon bayan wannan tsari.
Abdullahi ya ce mafi dacewa ga jam’iyyar shi ne su cimma matsaya ta bai daya domin rage kashe kudade da kuma kauce wa rikice-rikice.
Ya ce:
“Muna kokarin daukar tsarin maslaha domin shi ne mafi sauki a gare mu, kuma shi ne mafi alheri idan muka cimma yarjejeniya.”
Ya kuma soki jam’iyyar APC mai mulki, yana cewa karfinta ya dogara ne kacokan a kan shugabanta na yanzu.

Source: Twitter
Fatan da ADC ke yi wa APC
A cewarsa, idan aka cire iko daga APC, jam’iyyar ba za ta dawwama ba, domin shugaban kasa ne ke rike ta gaba daya.
Ya kara da cewa bayan Bola Tinubu ya bar mulki, jam’iyyar za ta watse cikin gaggawa fiye da yadda ake tsammani, cewar TheCable.
Abdullahi ya bayyana APC a matsayin wata jam’iyya da aka kirkira ne domin cimma wasu manufofi na musamman, ciki har da shugabancin Muhammadu Buhari da na Tinubu.
Ya ce jam’iyyar ADC ta kusan cika manufarta, kuma hakan na nuna dalilin da ya sa take cikin damuwa gabanin zabuka masu zuwa.
Ya tambaya dalilin da ya sa jam’iyya mai gwamnoni 31 da rinjaye a majalisar kasa ke nuna fargaba da kokarin raunana ‘yan adawa.
A karshe, ya ce a zabe mai gaskiya da adalci a Najeriya, APC ba za ta samu nasara ba, domin ‘yan Najeriya sun gaji da ita.
Kwankwaso ya kammala shirin komawa ADC
A baya, an ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kammala shirye-shiryen komawa jam'iyyar ADC domin fuskantar zaben shekarar 2027.
Kakakin kungiyar Kwankwasiyya ya bayyana cewa jagoran nasu fice daga jam'iyyar NNPP a hukumance a gidansa na kan hanyar Miller.
An ba dukkan mambobin Kwankwasiyya umarnin gaggawa na su garzaya mazabunsu domin yin rajista da jam'iyyar ADC.
Asali: Legit.ng

