A Karshe, Kwankwaso Ya Yi Murabus daga NNPP, Ya Jero Manyan dalilan Barinta
- Tsohon gwamnan Knao, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tabbatar da yin murabus daga daga jam’iyyar NNPP mai adawa
- Kwankwaso ya bayyana wannan mataki da ya dauka a matsayin mai wahala, yana mai cewa sauyin siyasa a kasa ya tilasta masa haka
- Rahotanni sun nuna cewa Kwankwaso na shirin komawa ADC inda ake sa ran zai bayyana matsayarsa a Kano nan ba da jimawa ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP mai adawa a Najeriya.
Jagoran siyasar Kwankwasiyya ya bayyana cewa yana bukatar sake daidaita tafiyar siyasarsa domin nasara a zaben 2027.

Source: Facebook
Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin Sanatan wanda ya wallafa a Facebook a yau Lahadi 29 ga watan Maris, 2026.
Musabbabin ficewar Kwankwaso daga NNPP
Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023 a karkashin jam’iyyar, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
A cikin rubutun da ya yi a Facebook, Kwankwaso ya ce:
“Ina sanar da ficewata daga jam’iyyar NNPP nan take."
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne bisa la’akari da yadda siyasar Najeriya ke tafiya a yanzu, wanda ke bukatar sabon tsari mai inganci.
Ya kara da cewa ya ga dacewar komawa wata dandalin siyasa da zai ba shi damar taimakawa wajen kawo sauyi a kasar yadda ya kamata.

Source: Facebook
Godiya da Kwankwaso ya yi ga NNPP
Kwankwaso ya gode wa shugabannin jam’iyyar, ciki har da shugabanta, Ajuji Ahmed, da sauran mambobi bisa goyon bayan da suka ba shi.
Haka kuma ya yabawa dukkanin shugabanni daga matakin kasa zuwa jiha da kuma gunduma, yana mai cewa sun taka muhimmiyar rawa a tafiyarsa.
Ya kuma yaba wa magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya tare da sauran masu goyon bayan jam’iyyar bisa jajircewarsu da goyon bayansu.
Kwankwaso ya ce za su ci gaba da hada kai domin gina kyakkyawar makoma ga Najeriya domin inganta rayuwar talakawa a kasar.
Sai dai bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba a hukumance, duk da cewa rahotanni sun nuna yana shirin shiga ADC.
Majiyoyi sun ce ana sa ran zai bayyana komawarsa sabuwar jam’iyya a Kano, inda manyan shugabannin jam’iyyar za su tarbe shi.
An kuma ruwaito cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya karbi bakuncin Kwankwaso a Abuja, inda suka tattauna kan halin da kasar ke ciki.
An fara hasashen tikitin Kwankwaso, Obi
Tun farko, kun ji cewa maganar hadakar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na kara daukar hankali yayin da APC ke ci gaba da karfafa iko.
Wasu na ganin hadakar za ta kawo sauyi a zaben 2027, yayin da wasu ‘yan siyasa ke cewa ba za ta zama barazana ga gwamnati ba.
Rahotanni sun nuna cewa ana tattaunawa a boye kan tikitin hadaka, amma har yanzu akwai sabani kan wanda zai yi jagoranci.
Asali: Legit.ng

