APC Tana cikin Matsala, Maganar Tikitin Kwankwaso da Obi Ya Fara Jan Hankali
- Maganar hadakar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na kara daukar hankali yayin da APC ke ci gaba da karfafa iko
- Wasu na ganin hadakar za ta kawo sauyi a zaben 2027, yayin da wasu ‘yan siyasa ke cewa ba za ta zama barazana ga gwamnati ba
- Rahotanni sun nuna cewa ana tattaunawa a boye kan tikitin hadaka, amma har yanzu akwai sabani kan wanda zai yi jagoranci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Rahotanni sun nuna cewa yiwuwar hadakar siyasa tsakanin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na kara haifar da farin ciki a tsakanin wasu ‘yan Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan shirin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na komawa ADC a ranar Litinin 30 ga watan Maris, 2026.

Source: Twitter
Ana hasashen ADC za ta APC mamaki
Rahoton Vangaurd na ganin wannan hadaka na iya zama kalubale ga APC mai mulki, wadda ke kara karfafa iko tun daga shekarar 2015.
A yanzu, APC na rike da mafi yawan jihohi da kujerun majalisa, lamarin da ke nuna yadda siyasa ke karkata zuwa bangare daya.
Rahoton ya ce wannan yanayi na iya rage gasa a siyasa tare da kara tasirin gwamnati a kan harkokin kasa baki daya.
A gefe guda, ana ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin ADC kan yiwuwar hadakar Obi da Kwankwaso.
An ce akwai sabani a farko kan iko da tsarin jam’iyya da kuma wanda zai zama shugaban tikitin zaben 2027.
Sai dai ana ganin an samu sassauci a wasu bangarori, amma har yanzu batun wanda zai jagoranci tikitin na nan a bude.

Source: Twitter
Tasirin da tikitin Kwankwaso/Obi zai yi
A baya, kokarin hada kan ‘yan takarar biyu kafin zaben 2023 ya ci tura sakamakon rashin jituwa kan mukami.
Wasu masu sharhi na ganin hadakar za ta iya zama mai karfi idan aka hada karfin matasa na Obi da tsarin siyasar Kwankwaso.
Sai dai wasu ‘yan siyasa sun rage tasirin hadakar, suna cewa ba za ta zama barazana ga shugaba Bola Ahmed Tinubu ba a zaben 2027.
Yadda Kwankwaso ke son ganin murmushin talaka
Kwankwaso dai ya sha fadin cewa babban abin da ya sanya a gaba shi ne ganin an samar wa talaka rayuwa mai inganci.
Ya sha sukar gwamnatin Bola Tinubu da APC kan yadda suka jefa yan Najeriya cikin mummunan hali inda ya ke shawartar yan kasar da su yi karatun ta natsu a zaben shekarar 2027.
Kwankwaso ya fara shirin kifar da Abba
Mun ba ku labarin cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya sake caccakar Gwamna Abba Yusuf kan butulce masa da ya yi bayan ya bar jam'iyyar NNPP ya koma APC gabanin 2027.
Kwankwaso ya bayyana cewa matakin sauya shekar gwamnan tamkar mutum ne ya dabawa kansa wuka, inda ya kira matakin da 'juyin kwakwalwa'.
Jagoran Kwankwasiyyar ya jaddada cewa Allah SWT ba zai bar wadanda suka ci amana ba, yayin da yake jaddada taken "falle daya ce" ga Abba a Kano.
Asali: Legit.ng

