Wike Ka Iya Bijirewa Tinubu a 2027, Ya Fadi Abin Mamaki da PDP Za Ta Yi
- Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya yi magana game da tasirin jam'iyyar PDP a zaben da za a yi a 2027
- Wike ya tabbatar da cewa taron jam’iyyar PDP mai adawa zai gudana kamar yadda aka tsara duk da rikice-rikicen cikin gida
- Ministan ya kara da cewa sulhu tsakanin ‘yan jam’iyya zai ci gaba bayan taron, yana jaddada cewa jam’iyyar tana kokarin hada kai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana tasirin da jam'iyyar PDP mai adawa za ta yi a zaben 2027.
Wike ya bayyana cewa taron kasa na jam’iyyar da aka shirya ranar 29 da 30 ga watan Maris, 2026 zai gudana kamar yadda aka tsara.

Source: Facebook
Nyesom Wike ya magantu kan rikicin jam'iyyar PDP
Wike ya ce duk da rikice-rikicen cikin gida, kokarin sulhu da wadanda ba su ji dadi ba zai ci gaba bayan kammala taron jam’iyyar, cewar TVC News.
Ya kuma bayyana cewa PDP za ta bai wa ‘yan Najeriya mamaki a zaben 2027, yana mai cewa jam’iyyar za ta nuna karfinta a zaben mai zuwa.
Ministan ya yi watsi da karar da wasu suka shigar a Kotun Koli, yana mai cewa hakan ba zai hana gudanar da taron ba.
Wike ya gano hanyar warware matsalar PDP
Da yake magana bayan duba wurin taron a Abuja, ya ce sulhu abu ne da ake ci gaba da yi a kowane lokaci a cikin jam’iyya mai yawan mambobi.
Ya kara da cewa an riga an raba mukamai bisa tsarin yankuna, inda aka ware shugabancin kasa zuwa Kudanci, yayin da shugabancin jam’iyya aka bai wa Arewa.
Wannan na zuwa ne yayin da jam'iyyar ke ci gaba da fama da rikicin cikin gida wanda ya jawo ficewar gwamnoni da jiga-jiganta zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Source: Facebook
Wike ya fadi shirin da PDP ke yi
Wike ya jaddada cewa wannan tsarin hadin kai zai taimaka wajen saukaka gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar.
Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar ta shirya sosai domin taron, yana mai cewa sun kai kusan kashi 95 cikin 100 na shiri kafin fara taron.
A cewarsa, an kammala shirye-shiryen zama na wakilai daga jihohi daban-daban, tare da tanadin wuraren manyan baki.
Ya kara da cewa ana sa ran kimanin wakilai 2,500 ne za su halarci taron da za a gudanar a ranakun Lahadi da Litinin, cewar Daily Post.
Wike ya gargadi Sanata Kingibe kan zabe
Mun ba ku labarin cewa Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sake takalo fada tsakaninsa da Sanata Ireti Kingibe.
Nyesom Wike ya bayyana cewa Ireti Kingibe ba za ta iya komawa kan kujerarta ba ta wakiltar Abuja a majalisar dattawan Najeriya.
Tsohon gwamnan ya zayyano hujjojinsa da suka sanya yake ganin sanatar wadda ba su ga maciji ba za ta kai labari ba a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

