Ja'oji: Ana tsakiyar Taron APC, 1 daga cikin Manyan Hadiman Tinubu Ya Yi murabus
- Nasir Bala Ja'oji, babban mai tallafa wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus, yayin da ake tunkarar kakar zaben 2027
- Yanzu haka magoya bayansa sun fara shirin gudanar da gangamin tarbar sa a jihar Kano domin ƙarfafa masa gwiwa kan burinsa na gaba
- Ana sa ran cewa Nasir Ja'oji zai ƙaddamar da gagarumin yaƙin neman zaɓe a hukumance, don neman kujerar dan majalisar tarayya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Nasir Bala Aminu wanda aka fi sani da Ja’oji ya yi murabus daga mukaminsa na babban hadimin shugaban kasa kan harkokin 'yan kasa da shugabanci a yau Asabar.
Tsohon hadimin ya yi murabus ne domin biyayya ga umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na cewa masu sha'awar neman takara su ajiye aikinsu.

Source: Facebook
Hadimin Tinubu ya yi murabus
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa Ja’oji yana hararar kujerar wakiltar mazabar Tarauni ta jihar Kano a majalisar wakilai ta kasa a shekarar yau.
Wannan mataki nasa yana zuwa ne kwanaki uku kacal kafin cikar wa'adin da shugaban ƙasa ya bayar ga dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa dake da burin takara a babban zaɓen 2027.
A cikin wasiƙar murabus ɗinsa, Nasir Ja’oji ya bayyana cewa ya sauka ne domin ya samu damar fuskantar siyasar dake gabansa biyo bayan umarnin Tinubu.
Tsohon hadimin ya nuna matuƙar godiya ga Shugaba Tinubu bisa yardar da ya nuna masa, har ya ba shi damar waƙiltar matasan Najeriya a matakin ƙasa.
Ja'oji zai nemi takarar d'an majalisar wakilai
Ya jaddada cewa naɗin nasa wata bayyananniyar shaida ce ta yadda wannan gwamnati take kishin matasa tare da ba su damar bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen gina ƙasa.
Duk da cewa Ja’oji bai fito fili ya bayyana muƙamin da yake nema ba, majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa yana hararar kujerar dan majalisar wakilai, na mazaɓar Tarauni ta jihar Kano.
Magoya bayansa a faɗin jihar Kano sun tarbi wannan labari da farin ciki, inda suka bayyana cewa lokaci ya yi da matashi kamarsa zai wakilci mutanen yankin.

Source: Twitter
Makomar siyasar Ja'oji a 2027
Nasir Ja'oji ya bayyana cewa matakin da ya ɗauka na murabus nuni ne na jarumta da kuma bin ƙa'idodin da shugabanci na gari ya shimfiɗa a faɗin Najeriya, in ji rahoton Daily Nigerian Hausa.
Yanzu haka magoya bayansa sun fara shirin gudanar da gangamin tarbar sa a jihar Kano domin ƙarfafa masa gwiwa kan wannan gagarumin buri na siyasa.
Ana sa ran cewa Nasir Ja'oji zai ƙaddamar da gagarumin yaƙin neman zaɓe a hukumance nan ba da daɗewa ba bayan ya kammala mika dukkan takardu na ofis.
Umarnin Tinubu ga mukarraban gwamnati
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya umarci dukkan ministoci da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa dake son yin takara a 2027 su yi murabus.
Wannan mataki ya biyo bayan tanadin Dokar Zaɓe ta 2026 domin tabbatar da adalci da hana amfani da muƙaman gwamnati wajen takara.
Dole ne dukkan ministoci da shugabannin hukumomin tarayya su mika wasiƙun murabus ɗinsu kafin ƙarshen watan Maris din 2026.
Asali: Legit.ng


