Gwamnoni 31, Wakilai sama da 8,000 Sun Hallara a Babban Taron APC a Abuja
- Wakilai sama da 8,000 ne za su hallara a filin wasanni na Eagle Square don zaben sababbin shugabannin jam'iyyar APC a yau
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a yi amfani da tsarin maslaha wajen zaben shugabannin da za su jagoranci jam'iyyar
- Ministan labarai, Mohammed Idris ya bukaci 'yan jam'iyyar da su nuna kishi da haɗin kai domin tabbatar da nasarar wannan taro
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Aƙalla wakilai 8,433 ne ake sa ran za su hallara a dandalin Eagle Square dake birnin Abuja domin gudanar da babban taron ƙasa na jam’iyyar APC na shekarar 2026.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zai jagoranci taron, tare da rakiyar gwamnoni 31 na jam’iyyar da kuma 'yan majalisar ministocinsa a tsakanin ranar 27 zuwa 28 ga watan Maris, 2026.

Source: Twitter
An shirya babban taron APC a Abuja
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a otal ɗin Transcorp Hilton dake Abuja, in ji rahoton Channels TV.
Mohammed Idris, wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin yaɗa labarai na taron, ya jaddada cewa wannan taro babban mataki ne ga jam’iyyar wajen ƙarfafa tsarin dimokiraɗiyya na cikin gida.
Ya yi kira ga mambobin kwamitin da su yi aiki tare cikin haɗin kai domin isar da saƙon jam’iyyar ga ‘yan Najeriya yadda ya kamata.
Wani babban labari da ya fito gabanin taron shi ne matsayar jam’iyyar na amfani da tsarin maslaha wajen zaɓen sababbin shugabannin da za su jagoranci tafiyar jam’iyyar.
APC za ta yi zabe ta hanyar maslaha
Mataimakiyar sakataren yaɗa labarai ta jam’iyyar, Mary Ikoku, ta tabbatar da hakan a ranar Laraba, inda ta bayyana cewa wannan tsari zai taimaka wajen kiyaye haɗin kan mambobi.

Kara karanta wannan
Turaki ya faɗa matsala: Kotu ta bada umarni a kamo shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa
Duk da cewa an amince da tsarin maslaha ga shugabannin jam’iyya, Ikoku ta bayyana cewa har yanzu jam’iyyar ba ta yanke shawarar yadda za a gudanar da zaɓen fitar da gwani na masu neman takara ba, domin hakan zai dogara ne da yanayin siyasar kowane yanki.
Wannan taro dai shi ne zai samar da shugabannin da za su shirya zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa, gwamnoni, da ‘yan majalisu gabanin babban zaɓen 2027.

Source: Twitter
Manyan jami’an gwamnati da suka hallara
Taron manema labaran ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo; Ministar al'adu, Hannatu Musawa; da kuma masu ba shugaban ƙasa shawara na musamman, Bayo Onanuga da Sunday Dare.
Waɗannan jami'ai sun jaddada bukatar nuna tarbiyyar siyasa irin ta Shugaba Tinubu yayin gudanar da taron, in ji rahoton Punch.
Ana ganin cewa nasarar wannan taro zai nuna ƙarfin APC da kuma irin shirin da take da shi na ci gaba da riƙe ragamar mulkin Najeriya.
'Yan kwangila na barazana ga taron APC
A wani labari, mun ruwaito cewa, kungiyar ƴan kwangila na cikin gida ta AICAN ta yi barazanar dirar mikiya a babban taron APC da aka shirya za a yi a Abuja.

Kara karanta wannan
Tinubu: Arewa ta Tsakiya ta gama shiri, ta fitar da 'dan takarar Shugaban kasa a 2027
Ƴan kwangila sun bayyana takaici a kan yadda hakkokinsu ke neman shiga mawuyacin hali duk da sun kammala aiki lafiya lau.
Ƙungiyar ta bayyana cewa ƴaƴanta na neman a biya su Naira biliyan 150 a cikin awa 48 daga bashin ayyukan gwamnati da suka aiwatar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
