2027: Atiku Ya Samu Goyon Baya a ADC, an Nuna Shi a Matsayin Dan Takara
- Yayin da ADC ke cigaba da yi wa mutane rajista, daya daga cikin manyan jam'iyyar, Dele Momodu ya nuna goyon baya ga Atiku Abubakar
- Cif Momodu ya bayyana haka ne yayin wata hira da 'yan jarida, inda ya ce ya kamata jam'iyyar ADC ta ba 'yan Arewa damar yin takara
- Hakan na zuwa ne yayin da manyan 'yan siyasa kamar Peter Obi, Rotimi Ameachi da sauransu ke nuna sha'awar yin takara a ADC a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Mawallafin mujallar Ovation kuma jigo a ADC, Dele Momodu ya bukaci jam’iyyar ta mika tikitin takarar shugaban ƙasa zuwa yankin Arewa a zaɓen 2027.
Ya yi maganar ne yayin da 'yan siyasa da dama daga Arewa da Kudu suka nuna sha'awar yin takara a matakai daban-daban a karkashin ADC.

Kara karanta wannan
Turaki ya faɗa matsala: Kotu ta bada umarni a kamo shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa

Source: Facebook
Shirin karawa da jam'iyyar APC a 2027
Da yake magana a ranar Laraba a shirin siyasa a tashar Arise TV, Momodu ya ce dole ne ADC ta dauki matakin tsara dabaru domin kayar da jam’iyyar APC a 2027.
“Shawarata ga ADC mai sauƙi ce: lokaci ya fara kure mana. Na taba neman takara sau biyu — a 2011 da 2023 — kuma na san cewa shugabanci ba wasa ba ne,”
Inji Momodu
Ya ce kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 ba ba abu ne mai sauki ba, yana mai cewa jam’iyyar na bukatar haɗin kai da da tsara tsari mai kyau.
Momodu ya ce ADC na da gogaggun ‘yan takara ciki har da fitattun ‘yan siyasa da suka fafata a zaɓen 2023, don haka bai kamata ta nuna kamar ita 'yar koyo ba ce.

Source: Facebook
Ya yi misali da dabarun siyasa da suka kai ga nasarar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a 2015, yana mai cewa ana cin zaɓe ne ta hanyar gina tsari da haɗin gwiwa.

Kara karanta wannan
Tinubu: Arewa ta Tsakiya ta gama shiri, ta fitar da 'dan takarar Shugaban kasa a 2027
Dele Momodu na so a ba Atiku takara
Da aka tambaye shi wanda yake so ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Momodu ya ce Atiku Abubakar ne zabin da ya ke da shi.
“Zabina shi ne Atiku. Ban taba ɓoye wannan ba,”
Inji shi.
The Cable ta rahoto cewa ya kuma shawarci ADC ta mai da hankali kan 'yan Arewa, inda ya ce mutane da yawa ba su jin dadin salon mulkin APC:
“A fannin dabaru, dole ADC ta je yankin da mutane ke da ƙorafi sosai kan APC.
"Mutanen da suka taimaka wa Tinubu ya zama shugaban ƙasa sun hada da mutanen Buhari. Yanzu suna cikin fushi da takaici saboda ana ganin an watsar da su,”
Legit ta tattauna da dan PDP
Wani dan jam'iyyar PDP a jihar Gombe, Bilyaminu Yahaya ya bayyanawa Legit Hausa cewa su har yanzu ba su san inda suka dosa ba game da takarar 2027.
Ya ce:
'Da yawa daga cikin wadanda muka zaba a baya sun sauya sheka, wasu ba su yi abin kirki ba, hakan ya kara jefa mu a matsala."
"Muna fatan lamura su daidaita domin ganin wanda ya kamata mu marawa baya a zaben 2027."
Atiku ya magantu kan Khalifa Zariya
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi kira ga gwamnatin Najeriya kan kama Sheikh Sani Khalifa Zariya.
Atiku ya bayyana cewa ya kamata a saki malamin ya koma cikin iyalan shi ko kuma a gurfanar da shi a gaban kotu idan yana da laifi.
Sanarwar da Legit Hausa ta samu ta nuna cewa tun a shekarar 2025 hukumomi suka kama Sheikh Khalifa saboda zargin alaka da masu yunkurin juyin mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
