Bayan Shigar Gwamna Dauda APC, Matawalle Ya Kinkimo Batun Takara a 2027

Bayan Shigar Gwamna Dauda APC, Matawalle Ya Kinkimo Batun Takara a 2027

  • Karamin Ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle, ya tabo batun aniyarsa ta yin takarar gwamnan jihar Zamfara a zaben 2027
  • Bello Matawalle ya bayyana cewa ya jingine burinsa na fafatawa da Gwamna Dauda Lawal don neman ragamar mulkin Zamfara
  • Karamin Ministan ya kuma nuna cewa a shirye yake ya ba da irin ta sa gudunmawar don ganin Gwamna Dauda ya samu tazarce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi magana kan yin takarar gwamnan jihar Zamfara a zaben 2027.

Bello Matawalle ya sanar da cewa ba zai tsaya takarar zaɓen gwamna na shekarar 2027 ba, domin ya marawa takarar neman tazarce ta Gwamna Dauda Lawal baya.

Matawalle ya hakura da takarar gwamna a 2027
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal da karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle Hoto: Dauda Lawal, Ibrahim Yusuf Danhausa
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Matawalle, Ahmad Dan-Wudil ya sanya a sahfinsa na Facebook a ranar Laraba, 25 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Matakin farko da alkali ya dauka a zaman shari'ar El Rufai da gwamnatin Najeriya

Me Matawalle ya ce kan takara a 2027?

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, tsofaffin gwamnoni da suka haɗa da Abdulaziz Yari, shugabannin APC, da sauran jiga-jigan jam’iyyar na jihar Zamfara.

Yayin da yake jawabi a wurin taron, Matawalle ya ce:

“Na janye aniyata ta tsayawa takarar zaɓen gwamna, kuma zan taimaka wa ɗan uwana Gwamna Dauda Lawal da dukkan zuciyata domin a sake zaɓensa a shekarar 2027.”

Kashim Shettima ya yi jawabi

Jaridar The Punch ta ce da yake jawabi ga dubban jama’a a wurin taron, mataimakin shugaban kasa Shettima ya jaddada ƙudurin gwamnatin tarayya na kawo ƙarshen ƙalubalen tsaro a jihar Zamfara.

Shettima ya ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta tura isassun jami’an tsaro da kayan aiki domin yaƙar 'yan bindiga yadda ya kamata.

Haka zalika, ya yi alƙawarin bayar da cikakken goyon baya ga kyakkyawan yunƙurin gwamnan na ciyar da jihar gaba.

Ya yi kira ga mazauna jihar da su sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu da gwamnan na Zamfara a babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Shirin gwamna na komawa APC ya jawo an fara gudun gwamnatinsa

“Gwamnatin tarayya za ta yi duk abin da za ta iya don ganin an kawar da ’yan bindiga masu addabar mutanen wannan jiha."
“Za mu ba wa Gwamna Dauda Lawal duk wani taimako da goyon baya da ya dace domin ya ci gaba da kyawawan ayyukan da ya fara."
“Ina kiran mutanen jihar nan da su sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dauda Lawal a babban zaɓen 2027."

- Kashim Shettima

Matawalle ya fasa takarar gwamna a 2027
Bello Matawalle, Dauda Lawal, Kashim Shettima da Abdul'aziz Yari Hoto: Almansoor Gusau
Source: Facebook

Abin da Matawalle ya ce kan tazarcen Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi magana kan tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Bello Matawalle ya bayyana cewa Tinubu zai samu nasara mai gamsarwa a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Ministan ya gargadi ‘yan siyasa da ke shiga shirye-shiryen makircin siyasa tun da wuri da kuma fafutukar karbe mulki, yana cewa irin wadannan dabaru na da illa ga kwanciyar hankalin dimokuradiyyar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng