An Zo Wajen: Gwamna Abba Ya Yi Magana kan Lokacin Cire Jar Hular Kwankwasiyya
- Ana ta muhawara kan ci gaba da sanya jar hular Kwankwasiyya da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke yi duk da komawa jam'iyyar APC
- Wasu na ganin lokaci ya yi da zai daina sanya jar hular tun da ya raba gari da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
- Mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi tsokaci kan lokacin da za a daina sanya jar hular ta Kwankwasiyya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan daina sanya jar hular Kwankwasiyya.
Gwamna Abba ya sake tabbatar wa magoya bayansa cewa zai ci gaba da sanya sananniyar jar hular nan ta Kwankwasiyya, duk da komawarsa jam’iyyar APC.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya a shafinsa na Facebook.
An ga Gwamna Abba ba jar hula
An dade ana samun rade-radin da ke karuwa a jihar game da kin cire hular da gwamnan ya yi, wadda take zaman babban alamar tafiyar Kwankwasiyya.
Sai dai, lokacin da aka gan shi sanye da wata hula mai wata kala daban ba ja ba wadda ke dauke da tambarin Tinubu a Yola, jihar Adamawa, wasu daga cikin magoya bayansa sun tambaya ko lokaci ya yi da za su iya jefar da jar hular.
Yaushe Abba zai cire jar hula?
Amma kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce har yanzu ba a ba da wani umarni na cire hular ba domin "lokacin yin hakan bai yi ba".
A cikin sakon da ya wallafa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce:
"Har yanzu ba a bayar da umarnin cire jar hula ba, wannan wata fita ce ta musamman a Yola ta jihar Adamawa da manyan baki suka yi anko."
"A jira, komai akwai lokaci....."
Ana ta muhawara kan sanya jar hular Abba
Wannan karin bayani ya zo ne yayin da mahawara ke kara zafi kan ci gaba da sanya jar hula da Gwamna Abba ke yi, alamar da aka dade ana dangantawa da tafiyar Kwankwasiyya karkashin jagorancin tsohon ubangidansa, Rabiu Musa Kwankwaso.

Source: Facebook
Duk da cewa Gwamna Abba ya nesanta kansa da manyan jiga-jigan Kwankwasiyya, ya rike jar hular a matsayin wani bangare na asalin siyasarsa.
Masu sharhi sun lura cewa hular ta wuce matsayin alamar siyasar bangaranci, ta zama wata alama ta al’adu a fadin jihar Kano.
A cikin 'yan kwanakin nan, da yawa daga cikin mabiyan Kwankwasiyya har ma da wasu magoya bayan gwamnan suna ta kiran gwamnan da ya cire hular, kamar yadda magajinsa, Abdullahi Ganduje, ya yi lokacin da suka raba gari da Kwankwaso a shekarar 2018.
Dalilin Abba na kin zuwa hawan Nasarawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin jihar Kano ta bayyana dalilin rashin ganin Gwamna Abba Kabir Yusuf a wajen hawan Nasarawa.
Gwamnatin ta bayyana cewa a al’adance, gwamnoni kan halarci wasu muhimman taruka na kasa musamman a lokacin bukukuwan Sallah.
A cewar gwamnatin, bikin Hawan Nasarawa ya zo daidai da wani muhimmin taron gwamnonin Najeriya, wanda hakan ya tilasta wa Gwamna Abba Yusuf fita daga jihar domin halartar taron.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


