Peter Obi Ya Ce an Kama 'Malamin Musulunci' da Ya Karbe Shi a Kaduna

Peter Obi Ya Ce an Kama 'Malamin Musulunci' da Ya Karbe Shi a Kaduna

  • Dan takarar shugaban kasa a 2023 a karkashin jam'iyyar LP, Peter Obi ya yi ikirarin kama malamin Musulunci da ya karbe shi a jihar Kaduna
  • Peter Obi ya bayyana cewa ya ziyarci mutumin da ya kira Sheikh Ahmad Tijjani Umar a ranar Lahadi, 22 ga watan Maris din shekarar 2026
  • Duk da cewa har zuwa lokacin hada rahoton, gwamnati ba ta yi bayani ba, wasu masu sharhi sun ce mutumin ba malami ba ne, dan siyasa ne

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, ya nuna damuwa bayan kama wani da ya ce malami ne da ya karɓe shi a Kaduna.

Wasu masu sharhi a kafafen sada zumunta, musamman daga jihar Kaduna sun nuna cewa mutumin yana da alaka da jam'iyyar ADC, ba malami ba ne.

Kara karanta wannan

Sabanin Mojtaba Khamenei, an fadi wanda Trump ke so ya jagoranci Iran

Ahmad Tijjani Umar da Peter Obi
Peter Obi da Ahmad Tijjani Umar da ya ziyarta a Kaduna. Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

Mutumin da Peter Obi ya ce an kama

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya ce an sanar da shi cewa jami’an tsaro sun kama malamin addinin, Sheikh Ahmad Tijjani Umar, jim kaɗan bayan ya karɓe shi a lokacin ziyararsa zuwa Kaduna.

Ya ce:

“Ina so in sanar cewa na samu labari da safiyar yau cewa an kama babban malamin addini, Sheikh Ahmad Tijjani Umar, an kama shi jim kadan bayan ya karɓe ni a Kaduna ranar Lahadi,”

Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya bayyana lamarin a matsayin alamar tabarbarewar ‘yancin ɗan adam, yana gargadin cewa hakan na iya kawo cikas ga dimokuraɗiyya idan ba a gaggauta magance shi ba.

“Wannan lamari na nuna yadda halin da ƙasar ke ciki yake ƙara muni, inda ‘yancin faɗar albarkacin baki ke cikin barazana, kuma ana cin zarafin ‘yan ƙasa da waɗanda ake kallon abokan hamayya na siyasa,”

Kara karanta wannan

Sheikh Mansur Sokoto ya yi wa Tinubu tsirara kan matsalolin Musulmi a Najeriya

Inji shi.

Magana kan 'yancin dan Adam

Obi ya jaddada cewa kare ‘yancin ɗan adam na da muhimmanci a kowace ƙasa mai dimokuraɗiyya, yana kira ga hukumomi da su bi doka wajen hulɗa da jama’a.

Daily Trust ta rahoto ya ce

“Dole ne ƙasar nan ta kare ‘yancin faɗar albarkacin baki, wanda shi ne ginshiƙin kowace dimokuraɗiyya. Danniya da tsoratarwa ba su da wuri a tsarin dimokuraɗiyya,”
Peter Obi da 'yan siyasa a Kaduna
Lokacin da Peter Obi ke jawabi a Kaduna. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

An ce dan siyasa ne ba malami ba

Wasu majiyoyi sun ce mutumin da aka kama mai suna Ahmad Tijjani Umar dan siyasa ne ba malami ba, sabanin bayanin Peter Obi.

Wani mai amfani da kafar X, Abubakar Yunusa ya wallafa cewa mutumin ne ya yi wa ADC takarar gwamna a jihar Kaduna a zaben 2023.

Lokacin da El-Rufai ya dawo Najeriya har aka yi yunkurin kama shi a fiin jirgi, Sheikh Ahmad Tijjani Umar ne suka ba shi kariya.

Kara karanta wannan

Dan jaridar Amurka ya yi ikirarin Netanyahu ya mutu har lahira

Gargadi kan tallata Tinubu a 2023

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Mansur Ibrahim Sokoto ya yi gargadi ga malamai game da tallata shugaba Bola Tinubu saboda addini a 2027.

Malamin ya bukaci masu shirin yi wa Tinubu kamfen, musamman malamai da su rika fadan ayyukan alheri da ya yi maimakon jingina shi ga addini kadai.

Farfesa Mansur Sokoto ya kara da cewa Musulmai ne mafi yawan wadanda suka zabi shugaba Bola Tinubu a 2023 amma an ware su a gwamnati.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng