Ta Faru Ta Kare, Jam'iyyar APC Ta Karbe Ikon Majalisar Dokokin Jihar Zamfara

Ta Faru Ta Kare, Jam'iyyar APC Ta Karbe Ikon Majalisar Dokokin Jihar Zamfara

  • Shugaban majalisar dokokin Zamfara da dukkan sauran mambobi sun sauya sheka daga PDP zuwa APC domin bin sahun Gwamna Dauda Lawal
  • Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne zai jagoranci taron karbar gwamna Dauda Lawal zuwa jam'iyyar APC a hukumance a gobe Talata
  • Jam'iyyar APC yanzu ita ke da dukkan kujeru 24 na majalisar dokokin jihar Zamfara bayan wannan gagarumin sauyin shekar na yau

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara, Bilyaminu Moriki, ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa jam'iyyar APC a yau Litinin.

Wannan gagarumin sauyin sheka ya faru ne tare da wasu mambobin majalisar 12, wadanda suka mika takardun yin murabus daga jam’iyyar tasu ta baya yayin zaman majalisar da aka gudanar a birnin Gusau.

Shugaban majalisa da 'yan majalisa 12 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Ginin majalisar dokokin jihar Zamfara da ke a birnin Gusau. Hoto: Zamfara State Assembly
Source: Facebook

APC ta karbe ikon majalisar jihar Zamfara

Kara karanta wannan

Ba wasa: Sojoji sun yi dirar mikiya a sansanin Bello Turji, an yi kazamin artabu

Wannan mataki ya biyo bayan sauya shekar da Gwamna Dauda Lawal ya yi kwanan nan daga PDP zuwa APC, a cewar rahoton Daily Trust.

Sakamakon wannan sabon lamari, jam'iyyar APC yanzu ita ce ke da dukkan kujeru 24 na majalisar dokokin jihar, wanda hakan ke nufin PDP ba ta da ko wakili daya a majalisar a halin yanzu.

Shugaban majalisar, Moriki, ya bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne domin su mara wa Gwamna Dauda Lawal baya wajen ciyar da jihar gaba.

A cewarsa, sun tuntubi mutanen mazabunsu kuma sun sami goyon baya kafin su yanke shawarar barin PDP.

Jiga-jigan majalisa da suka sauya sheka

Ya kara da cewa tafiyarsu zuwa APC za ta taimaka wajen samar da kyakkyawar alaka tsakanin gwamnatin jiha da ta tarayya domin amfanin al'ummar Zamfara.

Daga cikin manyan jami'an majalisar da suka sauya shekar har da Mataimakin Shugaban Majalisa, Adamu Aliyu; Shugaban Masu Rinjaye, Bello Mazawaje; da kuma babban mai tsawatarwa na majalisar, Rilwanu Nagambo.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa ta ware gobe Talata, 24 ga Maris, 2026, domin karbar Gwamna Lawal a hukumance.

Kara karanta wannan

A hukumance, Kashim Shettima zai karbi gwamnan da ya sauya sheka zuwa APC

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne zai karbi Gwamna Dauda Lawal zuwa APC
Taswirar jihar Zamfara da ke a Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An shirya tarbar gwamnan Zamfara zuwa APC

Ana sa ran Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ne zai jagoranci taron karbar gwamnan tare da shugabannin jam’iyyar na kasa da kuma tsofaffin gwamnonin jihar Zamfara.

Haka zalika, za a karbi dukkan sauran mambobin majalisar dokokin da suka sauya shekar tare da gwamnan a gobe, wanda hakan zai kawo karshen tasirin jam'iyyar PDP a manyan matakan siyasar jihar ta Zamfara a halin yanzu.

Zamfara: Ana ruguza allunan tallar Tinubu

A wani labari, mun ruwaito cewa, APC mai mulki a Najeriya ta yi gargadi game da zargin ruguza allunan tallan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a sassan Zamfara.

Kakakin APC a jihar Zamfara, Yusuf Idris Gusau ne ya fitar da sanarwa yana gargadin cewa ba za su taba lamuntar lalata musu kayayyaki ba.

A bayanin da ya fitar, Yusuf Idris Gusau ya sanar da cewa a baya sun mika korafi ga jami'an tsaro amma duk da haka ba a daina musu barna ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com