‘Arewa Na Bukatar Wakilci’: Gwamna Ya Fadi Yadda Ake Matsa Masa Ya Nemi Sanata

‘Arewa Na Bukatar Wakilci’: Gwamna Ya Fadi Yadda Ake Matsa Masa Ya Nemi Sanata

  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya yi karin haske kan yiwuwar tsayawa takarar sanata a zaben 2027
  • Gwamnan ya ce shugabanni da masu ruwa da tsaki sun bukace shi ya fito domin samar da ingantaccen wakilci
  • Ya bayyana cewa yana tuntubar masu ruwa da tsaki kafin yanke hukunci na ƙarshe kan tsayawa takara

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lafia, Nasarawa - Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan yiwuwar tsayawa takarar sanata bayan kammala wa'adinsa.

Abdullahi Sule ya bayyana cewa akwai yiwuwar ya tsaya takarar Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Arewa a zaɓen 2027 mai zuwa.

Gwamna ya ce an matsa masa ya nemi sanata
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa. Hoto: Gov. Abdullahi Sule Mandate.
Source: Facebook

Daily Trust ta ce Sule ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da mambobin majalisar zartarwar jiharsa suka kai masa a gidansa da ke Gudi a ƙaramar hukumar Akwanga.

Kara karanta wannan

Zai shiga APC ne? Sule Lamido ya bude kofar ganawa da Shugaba Bola Tinubu

Yadda ake matsa wa gwamnan ya fito takara

Sule ya ce ana matsa masa lamba daga shugabanni da masu ruwa da tsaki domin ya fito takara, yana mai cewa hakan na da muhimmanci wajen samar da ingantaccen wakilci ga yankin Arewa.

“Duk da matsin lamba da muke samu daga shugabanninmu, ba na son su ji cewa ban mayar da martani ba, ina musu alƙawarin zan tsaya takara idan lokaci ya yi."

Ya ƙara da cewa tun da farko yana da niyyar mara wa wani dan takara baya, amma ya sauya shawara bayan mutumin ya shiga cikin masu kira gare shi ya fito takara.

An fara matsawa gwamnan Nasarawa ya nemi takarar sanata
Taswirar jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Gwamna Sule ya fara tuntubar al'ummar Nasarawa

Gwamnan ya jaddada cewa yana ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki, ciki har da sarakunan gargajiya da manyan ‘yan siyasa daga Nasarawa ta Arewa, kafin yanke hukunci na ƙarshe.

Ana sa ran Sule zai bar mulki bayan kammala wa’adin mulkinsa na shekaru takwas a matsayin gwamna a ranar 29 ga watan Mayun 2027, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Hadimin gwamna ya yanke jiki ya fadi, ya mutu a wurin taro

A nasa bangaren, mataimakin gwamnan, Dakta Emmanuel Akabe, ya sake jaddada goyon bayan majalisar zartarwa ga gwamnan, yana mai cewa za su ci gaba da mara masa baya har zuwa ƙarshe.

“Za mu yi tafiya tare da kai har sai mun kai ga ƙarshe, sannan gaba ɗaya mu yi ihu da murna mu ce: mun zo, mun mamaye su, mun yi nasara.”

- Abdullahi Sule

Duka wannan na zuwa ne yayin da wasu gwamnoni ke shirin kammala wa'adinsu na biyu a kan kujerar gwamna wanda mafi yawansu za su nemi takarar sanata a zaben 2027.

Dan Lafia ya yi magana da Legit Hausa

Wani mazaunin birnin Lafia a jihar Nasarawa, Amin Abdullahi AT ya bayyana goyon bayansa ga takarar Abdullahi Sule.

Ya ce gwamnan ya kawo ababan more rayuwa yayin mulkinsa wanda ake sa ran zai ci gaba da abin alheri.

Ya ce:

"Kamar ni, ina goyon bayan tsayawarsa takarar sanata a majalisar dattawa bayan kammala mulki saboda zaton alherin da ake yi masa."

Gwamna Sule ya fadi karfin APC a Najeriya

An ji cewa Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce jam’iyyar APC a buɗe take ga ƙarin gwamnonin jihohi da ke son sauya sheƙa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Harin bam a Borno: Sanata Ndume ya faɗawa Tinubu abin da ya kamata ya yi

Abdullahi Sule ya bayyana a wancan lokaci cewa jam'iyyar APC ta karɓi gwamna na 29 mai ci a ofis, yayin da wasu ke shirin shiga jam’iyyar a nan gaba kaɗan.

A hirar da ya yi da manema labarai, gwamnan ya ƙaryata zargin cewa yawaitar gwamnonin APC na iya jefa Najeriya cikin tsarin jam’iyya ɗaya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.