Gwamna Ya Yi Jirwaye Mai Kama da Wanka kan Shiga APC, Ya Fadi Shirin da Suke Yi

Gwamna Ya Yi Jirwaye Mai Kama da Wanka kan Shiga APC, Ya Fadi Shirin da Suke Yi

  • Gwamna Bala Mohammed ya magantu kan rade-radin komawa APC, yana cewa zai ci gaba da zama a PDP duk da matsalolin da ke cikinta
  • Ya ce siyasa na iya sauyawa, amma za su dauki matakai cikin hikima da dabara ba tare da yin kuskure ba
  • Gwamnan ya yi alkawarin biyan albashi kan lokaci da kuma warware basussukan giratuti kafin ya kammala wa’adin mulkinsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yi karin haske yayin da ake ta yada cewa zai koma APC a Najeriya.

Wannan jita-jita na zuwa ne bayan kusan dukan gwamnonin PDP a Najeriya sun sauya sheka zuwa APC mai mulkin Najeriya.

Gwamna Bala ya yi magana kan jita-jitar APC
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi a gidan gwamnati. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed.
Source: Twitter

Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin @emmaikumeh wanda ya wallafa bidiyon a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Yadda rade radin mutuwar Netanyahu ke karuwa duk da bayyanar shi a bidiyo

Gwamna Bala ya magantu kan rade-radin komawa APC

Gwamna Bala ya tabbatar da cewa akwai matsaloli a PDP kamar yadda kowa ya sani amma dai ita siyasa komai na iya faruwa.

Ya tabbatar da cewa ba zai je ko ina ba duk da tarun matsalolin da ke cikin PDP inda ya ce za su iya kasancewa a ko ina amma dai cikin dabara ba za su bari kansu ya yi murfi ba.

Ya ce:

“Akwai jita-jitar cewa na koma APC. Ba zan je ko’ina ba, amma muna da matsaloli a PDP. Siyasa abu ne mai iya sauyawa.
"Za mu iya kasancewa a ko’ina, amma ba za mu yi wauta ba. Za mu dauki dukkan matakai cikin dabara.”
Gwamna ya sha alwashin inganta walwalar ma'aikata
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed.
Source: Twitter

Alkawarin Gwamna Bala ga ma'aikata a Bauchi

Gwamnan har ila yau, ya sha alwashin biyan albashi a kan lokaci da kuma tabbatar da biyan giratuti kafin kammala wa'adin mulkinsa a jihar Bauchi.

Bala Mohammed ya shawarci ma'akatan gwamnati da su yi aiki tukuru domin tallafawa gwamnati saboda samar da ababan more rayuwa.

Kara karanta wannan

"Ba za a ga watan Shawwal da idanu ba": Masani ya yi magana ana shirin Sallah

"Ina kira ga ma'aikatan gwamnati da sauran masu rike da mukaman gwamnati da mu yi amfani da abin da muke da shi a kasa yadda ya dace.
"Za mu ci gaba da samar da ababan more rayuwa ga al'umma domin samar da rayuwa mai inganci.
"Na yi alkawarin kafin na bar mulki zan yi kokari na biya dukan basukan da na gada na giratuti ga tsofaffin ma'aikata."

- Gwamna Bala Mohammed

An yi ta yada Gwamna Bala zai koma APC

A baya, mun sanar da ku cewa wasu majiyoyi sun ce Gwamna Bala Mohammed ya kammala shirin barin PDP zuwa APC a bayan tattaunawa da Shugaba Bola Tinubu kan makomarsa.

An ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya gargaɗi Bala Mohammed cewa ba zai ba shi ikon zaɓar wanda zai gaje shi ba koda ya koma jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

An kuma umarci Gwamna Bala ya ba ɗan shugaba ƙasa Seyi Tinubu haƙuri kafin a amince da buƙatarsa ta shiga cikin jam'iyyar mai mulki a ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.