Zaɓen 2027 Ya Matso: Shugaba Tinubu Ya Umarci Ministoci, Hadimai Su Yi Murabus
- Shugaba Bola Tinubu ya umarci dukkan ministoci da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa dake son yin takara a 2027 su yi murabus
- Wannan mataki ya biyo bayan tanadin Dokar Zaɓe ta 2026 domin tabbatar da adalci da hana amfani da muƙaman gwamnati wajen takara
- Dole ne dukkan ministoci da shugabannin hukumomin tarayya su mika wasiƙun murabus ɗinsu kafin ƙarshen watan Maris
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya umarci dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatinsa da ke da niyyar tsayawa takara a zaɓen 2027 su ajiye aiki kafin ranar 31 ga Maris, 2026. Wannan umarni ya shafi kowane mataki, kama daga muƙarrabai, hadimai da kuma shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya.

Source: Twitter
Wannan mataki, yana kunshe ne a cikin wata takardar umarni da aka fitar daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), a cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan
Duk da ba ya Najeriya, Zulum ya aiko da sako bayan tagwayen bama bamai a Maiduguri
Takardar ta ce umarnin ya yi daidai da tanadin Sashe na 88(1) na Dokar Zaɓe ta shekarar 2026, da kuma jadawalin gudanar da zaɓukan fitar da gwani na jam’iyyu da hukumar INEC ta fitar.
Wadanda Tinubu ya ba umarni su yi murabus
Takardar umarnin, wacce sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa dole dukkan ministoci, da ma’aikata da za a zayyana ƙasa dake son shiga takara su ajiye aiki:
- Ministoci: Manya da ƙananan ministoci
- Hadimai: Masu ba da shawara na musamman, manyan masu taimaka wa na musamman, mataimaka na musamman, da mataimaka na kashin kai.
- Shugabannin hukumomi: Manyan daraktoci, shugabannin gudanarwa na dukkan ma'aikatu, hukumomi, kwamishinoni, da kamfanonin gwamnatin tarayya.
- Da duk wani mai riƙe da muƙamin siyasa da shugaban ƙasa ya naɗa.
Dalilin Tinubu na bada wannan umarn
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa wannan mataki ya zama dole domin tabbatar da bin dokokin zaɓe sau da ƙafa, da kuma wanzar da gaskiya da adalci a cikin tsarin siyasa.

Source: Twitter
Manufar ita ce a samar da yanayi mai kyau ga dukkan masu neman takara ba tare da wani ya yi amfani da muƙaminsa na gwamnati wajen danne wasu ba in ji rahoton The Cable.
Haka zalika, shugaban ya sake nanata ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa dimuƙuradiyya da kuma tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zaɓe a ƙasar nan.
Ya buƙaci dukkan jami’an da abin ya shafa su tabbatar sun mika wasiƙun murabus ɗinsu ta ofishin SGF kafin cikar wa'adin da aka ɗiba.
Minista ya ƙaryata shirin takarar gwamna
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ministan labarai Mohammed Idris ya karyata rahoton cewa zai tsaya takarar gwamnan Neja a 2027.
Alhaji Mohammed Idris ya dakatar da hadiminsa, Sa’idu Enagi wanda shi ne ya wallafa rubutun da ke yawo game da batun takararsa.
A wata sanarwa da ministan ya wallafa a shafukansa na sadarwa, ya bayyana irin alakar da ke tsakaninsa da Gwamna Umaru Bago.
Asali: Legit.ng
