"Gaskiyar Dalilin da Ya Sa na Bar PDP na Shiga APC," Gwamna Dauda Ya Yi Bayani

"Gaskiyar Dalilin da Ya Sa na Bar PDP na Shiga APC," Gwamna Dauda Ya Yi Bayani

  • Gwamna Dauda Lawal ya bar jam'iyyar PDP ya koma APC domin samar da hadin kai wajen tunkarar matsalar rashin tsaro a jihar Zamfara
  • Mukaddashin Gwamna Mani Mummuni ya bayyana cewa rikicin cikin gidan PDP ya taimaka wajen tura gwamnan zuwa jam'iyya mai mulki ta APC
  • Yawan gwamnonin APC ya karu zuwa 31 bayan sauyin shekar Gwamna Dauda Lawal wanda hakan ya karfafa ikon jam'iyyar a fadin Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya girgiza fagen siyasar Najeriya bayan ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP tare da komawa jam'iyyar APC mai mulki.

Muƙaddashin gwamnan jihar, Malam Mani Mummuni, ne ya sanar da wannan mataki a madadin gwamnan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a fadar gwamnati dake birnin Gusau.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Gwamna Dauda Lawal ya bi sahun Abba Gida Gida, ya sauya sheka zuwa APC

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana dalilin fiewa daga PDP zuwa APC.
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC. Hoto: @daudalawal_/X
Source: Twitter

Gwamna Dauda Lawal ya shiga APC

Wannan babban sauyi na zuwa ne bayan gudanar da doguwar tuntuɓa da manyan masu ruwa da tsaki, shugabannin siyasa, dattawa da kuma magoya baya dake sassa daban-daban na Jihar Zamfara, in ji rahoton The Nation.

Malam Mummuni ya bayyana cewa rikicin cikin gida dake ƙara ruruwa a cikin jam'iyyar PDP da kuma buƙatar samar da haɗin kai mai ƙarfi domin tunkarar ƙalubalen tsaro da ci gaban jihar su ne manyan dalilan wannan sauyin sheka.

Masu ruwa da tsaki a taron da aka gudanar a babban ɗakin taro na Rescue Hall, sun ba gwamnan shawarar ya fito fili ya rungumi ajandar Renewed Hope ta gwamnatin tarayya.

Wannan zai ba Zamfara damar amfana sosai daga haɗin gwiwa da fadar shugaban kasa, musamman wajen samun tallafi da dabarun yaƙi da ƴan fashin daji dake addabar jihar.

Burin Gwamna Dauda bayan shiga APC

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Boko Haram ta kwace gari guda a Borno, an ji halin da ake ciki

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa ko da yake yana godiya ga mambobin PDP kan goyon bayan da suka ba shi a shekarun baya, yanayin siyasar yanzu ya tilasta masa ɗaukar wannan babban mataki domin kyakkyawan shugabanci da kyakkyawar makomar jihar Zamfara.

Ya jaddada cewa babban burinsa shi ne kawo ƙarshen rashin tsaro da kuma haɓaka tattalin arzikin jihar ta hanyar yin aiki kafa-da-kafa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

A cewarsa, wannan matakin zai ƙarfafa haɗin kai tsakanin jihar da tarayya wajen aiwatar da manufofin dake samar da ci gaba cikin gaggawa yau, in ji rahoton Punch.

Gwamna Dauda Lawal ya ce ya shiga APC don ganin an magance matsalar tsaro da tattalin arzikin jihar.
Taswirar jihar Katsina da ke a Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamnonin APC sun koma 31

Muƙaddashin Gwamnan ya kuma yi kira ga dukkan magoya bayan gwamnan da daukacin al'ummar jihar da su gaggauta yin rajista da APC, musamman a wannan lokaci da jam'iyyar take gudanar da aikin rajista na yanar gizo.

Ficewar Dauda Lawal ya sanya yawan gwamnonin APC ya tashi zuwa 31 a faɗin Najeriya, lamarin da ya ƙara ƙarfafa ikon jam'iyyar a fagen siyasar ƙasar.

Wannan sauyin sheƙa ya bar jam'iyyar PDP cikin hali na dar-dar, yayin da APC ke ci gaba da mamaye jihohin ƙasar a daidai lokacin da ake fuskantar wasu manyan zaɓuka nan gaba.

Kara karanta wannan

Ana jiran hukuncin babbar shari'ar da za ta bayyana makomar jam'iyyar PDP

Gwamnoni 2 da ake hasashen za su bar PDP

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki a kasa tare da mukarrabansa.

Haka kuma ana zaton bayan Dauda Lawal, akwai wasu gwamnonin PDP biyu da za su fice daga PDP, ana ganin daya d sha cikinsu zai koma APC.

Rikicin cikin gida a PDP ya jefa jam’iyyar cikin wani yanayi mai sarkakiya, lamarin da ya sa wasu gwamnoni ke duba yiwuwar wasu zabuka na siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com