Za a Shiga Takarar Gwamna, Ba a Ga Sunan Jam'iyyun LP da PDP cikin Masu Fafatawa ba

Za a Shiga Takarar Gwamna, Ba a Ga Sunan Jam'iyyun LP da PDP cikin Masu Fafatawa ba

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta bayyana jerin ‘yan takara da ta amince za su fafata a zaben Osun mai zuwa
  • Yayin da jam'iyyun ke shirin a fafata da su, an lura cewa babu manyan jam'iyyun adawa a Najeriya da suka hada da PDP da LP
  • Jam’iyyun siyasa 14 ne kawai suka kammala tsarinsu na zaben fitar da gwani da ake sa ran za su shiga zaben watan Agusta, 2026.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen ‘yan takara da za su fafata a zaben gwamna a jihar Osun.

Shiri ya kusan kammala domin tunkarar zaben da za a gudanar a ranar 8 ga Agusta, 2026 a Jihar Osun, inda za su sake zabar gwamna.

Kara karanta wannan

An fara: Tsohon gwamna ya shiga ADC bayan kai masa hari da kona ofishinta

INEC ta fitar da yan takarar gwamna a Osun
Farfesa Joash Amupitan, Shugaban INEC a Najeriya Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa a wani bayani da Musa Olurode, jami’in hulda da jama’a na INEC a Osun ya fitar ranar Juma’a, an amince da ‘yan takara daga jam’iyyun siyasa 14 su shiga zaben.

Shirin zaben Gwamnan Osun ya kankama

Daily Post ta wallafa cewa Olurode ya bayyana cewa jerin sunayen jam’iyyun da suka samu izini sun hada da jam'iyyu 14.

Sun hada da: Jam'iyyar A, AA, AAC, ADC, ADP, APGA,APC, APM, APP, BP, NNPP, PRP, YPP, da ZLP.

Sai dai Olurode ya kara da cewa jam’iyyun PDP da LP ba su samu shiga jerin ba. Wannan na nuni da cewa wasu manyan jam’iyyun sun fuskanci kalubale wajen fitar da yan takara.

Olurode ya ce fitar da jerin sunayen ‘yan takara na karshe ya yi daidai da tsarin aiki da jadawalin da INEC ta sanya wa zaben gwamna, inda aka tsara dukkan matakai kafin ranar kada kuri’a.

Kara karanta wannan

An nemi Na'ibin limami da wasu mazauna Katsina an rasa bayan hare haren yan ta'adda

Jam'iyyun da suka kammala shirin zaben Osun

A cikin watan da ya gabata, ya bayyana cewa jam’iyyun siyasa 14 ne kawai suka kammala gudanar da zabukan fitar da gwani yadda ya kamata.

Ya ce hakan na nuni da cewa zaben gwamna a Osun zai kasance na gaske da tsari mai kyau, tare da bayyana wadanda za su fafata a matakin zaben bisa tsari.

Wasu jam'iyyu sun gagara fitar da dan takara a zaben fitar da gwani
Taswirar jihar Osun inda aka shirya zaben gwamna a Agusta Hoto: Legit.ng
Source: Original

Hukumomi da masu ruwa da tsaki na fatan zaben zai gudana cikin lumana, kuma ‘yan kasa za su samu damar kada kuri’a bisa gaskiya da adalci.

A watan da ya gabata, Musa Olurode ya bayyana cewa jam’iyyun siyasa 14 ne kawai suka samu nasarar kammala zabukan fitar gwani tare da ɗora sunaye da cikakkun bayanan.

Gwamnan Osun ya ba da umarni

A baya mun wallafa cewa Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya gargadi duk masu shirin kutsawa ko karbe ikon fadar Ikirun Sarki ba bisa ka’ida ba.

Gwamnan ya umurci jami’an tsaro da su gaggauta kewaye wa da kare fadar domin hana duk wani tayar da hankali da zai jawo matsala da rashin kwanciyar hankali.

Gwamna Ademola Adeleke ya ce fadar Ikirun za ta ci gaba da kasancewa a kulle har sai kotu ta kammala shari’ar sarautar Akirun da ke gabanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng