Aminu Gwarzo: Matakai 8 da Majalisar Kano Za Ta Bi don Tsige Mataimakin Gwamna

Aminu Gwarzo: Matakai 8 da Majalisar Kano Za Ta Bi don Tsige Mataimakin Gwamna

Kano - A yau Alhamis, wani rahoto ya karade kafafen sadarwa na zamani dake cewa Majalisar Dokokin Kano ta tsige mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Sai dai, mai magana da yawun majalisar, Kamaluddeen Shawai, ya fito ya karyata wannan bayani, inda ya bayyana cewa abin da ya faru kawai shi ne gabatar da mataki na farko na tsigewar.

Majalisar Kano ta fara gudanar da matakan tsige mataimakin gwamnan Kano
Zauren majalisar dokokin jihar Kano yayin da ake zaman majalisa. Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Source: Facebook

A zantawarsa da Legit Hausa, Shawai ya nanata cewa akwai banbanci tsakanin gabatar da tuhuma da kuma tsige mutun daga mukaminsa.

Hakikanin abin da ya faru a majalisa

A cewar Kamaluddeen Shawai, abin da ya faru a zauren majalisar shi ne gabatar da takardar tuhuma guda hudu dake da alaka da hada-hadar kudade wadanda ake zargin mataimakin gwamnan da su.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Mataimakin gwamnan Kano na tsaka mai wuya, Majalisa ta tura masa sako

Ya bayyana cewa wannan mataki ne na farko a cikin jerin matakai daban-daban da kundin tsarin mulkin Najeriya ya shimfida kafin a kai ga tsige babban jami'in gwamnati.

Shawai ya kara da cewa rahotannin dake cewa an riga an tsige shi "kagaggun labarai ne" wadanda ba su da tushe yanzu.

"Abin da ya faru a zauren majalisar dokokin Kano a yau shi ne abin da ake cewa, gabatar da takarda ta tuhume tuhume, wadanda ake yi wa mataimakin gwamnan jihar Kano, amma ba wai an tsige mataimakin gwamnan ba.
"Kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanadi wasu matakai daban daban wanda za a iya kai wa ga tsige mataimakin gwamnan jihar Kano.
"Tuhume tuhume ne kusan akalla guda hudu, wadanda suke da jibanci da harkokin hada hadar kudi."

- Kamaluddeen Shawai.

Matakan tsarin mulki da kare kai

Mai magana da yawun majalisar ya yi bayanin cewa kundin tsarin mulki ya bai wa mataimakin gwamna damar kare kansa a tsakanin mako guda zuwa mako biyu bayan an gabatar da tuhume-tuhumen.

"Gazawar (mataimakin gwaman na kare kansa) zai sanya a je mataki na biyu. Idan aka kammala mataki na biyu, sai a tsallaka zuwa mataki na uku."

Kara karanta wannan

Majalisar dokoki ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan Kano, Aminu Gwarzo

- Kamaluddeen Shawai.

Shawai ya jaddada cewa tsige gwamna ko mataimakinsa babban al'amari ne dake bukatar bin matakai daki-daki, ciki har da shigar babban alkalin jihar da kuma kafa kwamitin amantattu kafin a kammala komai.

Wannan bayani ya zo ne domin kwantar da hankulan al'umma da kuma karkata hankalin mutane ga hakikanin tsarin shari'a dake gudana a majalisar, in ji rahoton Premium Times.

Kamaluddeen Shawai ya ja kunnen masu yada labaran karya da su kiyaye, inda ya ce yanzu aka fara matakin farko na bincike kan zarge-zargen da ake wa Aminu Gwarzo.

Matakan tsige mataimakin gwamna a Najeriya

Matakan da majalisar Kano za ta bi domin tsige mataimakin gwamnan jihar.
Aminu Gwarzo, mataimakin gwamnan Kano da majalisa ke shirin tsige wa. Hoto: Kwankwasiyya Repoters.
Source: Facebook

A daidai lokacin da dambarwar siyasa ke faruwa a Kano, yana da matuƙar muhimmanci al'umma su fahimci cewa tsarin mulkin Najeriya ya shimfiɗa matakai masu tsauri kafin a tsige gwamna ko mataimakinsa daga muƙami.

Sashe na 188 na kundin tsarin mulki shi ne ya fayyace waɗannan matakai daki-daki domin tabbatar da adalci da bin doka.

Kara karanta wannan

Malamai a siyasa: Sheikh Abdulmuddalib zai nemi gwamnan Zamfara a 2027

1. Gabatar da takardar zargi:

Dole ne akalla kashi ɗaya bisa uku na mambobin Majalisar Dokokin Jiha su rattaba hannu kan takardar da ke zargin mataimakin gwamna da aikata babban laifi.

Babban laifi (Gross Misconduct) a nan yana nufin keta kundin tsarin mulki ko aikata laifin da 'yan majalisa suka tsayu a kan ra'ayin cewa ya dace a tsige mutum a kansa.

2. Isar da takarda:

Shugaban Majalisa yana da kwanaki bakwai ya tabbatar da cewa mataimakin gwamna da kowane ɗan majalisa sun sami kwafin takardar da ke kunshe da wannan zargin.

3. Martanin mataimakin gwamna:

Mataimakin gwamna yana da haƙƙin rubuta raddi ga zarge-zargen, kuma dole ne a rarraba raddin ga kowane ɗan majalisa.

4. Kada kuri'ar bincike:

A cikin kwanaki 14, majalisa za ta kaɗa ƙuri'a ba tare da muhawara ba domin amincewa ko za a binciki mataimakin gwamna. Dole ne kashi biyu bisa uku na dukkan mambobi su amince.

Kara karanta wannan

An kama wanda ke tono kabari yana cire sassan gawa a watan Ramadan

5. Kafa kwamiti:

Idan majalisa ta amince, shugaban majalisa zai nemi Babban Alƙalin jihar ya kafa kwamitin mutum bakwai masu gaskiya waɗanda ba ’yan siyasa ba ne ko ma’aikatan gwamnati domin bincikar zargin.

6. Bincike da kare kai:

Kwamitin yana da watanni uku ya kammala aiki. A nan, mataimakin gwamna yana da haƙƙin kare kansa da kansa ko ta hannun lauyoyi.

7. Tabbatar da laifi:

Idan kwamitin ya ga ba a tabbatar da laifin ba, magana ta ƙare. Idan kuma an tabbatar da laifin, to za a gabatar da rahoton ga majalisa.

8. Matakin karshe:

Majalisa za ta yi la’akari da rahoton, idan kashi biyu bisa uku na dukkan mambobi suka kaɗa ƙuri’ar amincewa da rahoton, to mataimakin gwamna zai sauka daga mulki nan take.

An mikawa Gwarzo takardar tuhuma

A wani labari, mun ruwaito cewa, majalisar dokokin Kano ta fara bin matakan da doka ta tanada da nufin tsige mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo.

Kara karanta wannan

Ta zo gidan sauki: Tinubu ya fadi abin da za a tallata shi da shi a zaben 2027

Rahoto ya nuna cewa Majalisar jihar ta sanar da Aminu Gwarzo shirinta na tsige shi a wata takarda da ta aika ofishinsa yau Alhamis, 5 ga Maris, 2026.

Takardar na kunshe da duka tuhume-tuhumen da Majalisar take yi masa, wanda ya kunshi amfani da mukaminsa ta hanyar da ba ta dace ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com