Akwai Yiwuwar Tsohon Ministan Tinubu Ya Yake Shi, Yana Kus Kus da Kusoshin Adawa

Akwai Yiwuwar Tsohon Ministan Tinubu Ya Yake Shi, Yana Kus Kus da Kusoshin Adawa

  • Duk da musantawa da ya yi, ana kara samun kwararan alamu da ke nuna cewa tsohon Ministan tsaro Muhammed Badaru Abubakar zai bar APC
  • A baya-bayan nan, Muhammed Badaru ya gana da Sule Lamido da ɗansa Mustapha Lamido a gidansa, lamarin da ya ruruta wutar sauya sheka
  • Haka kuma, rashin halartarsa babban taron jam’iyyar APC na kasa da aka yi jihar Jigawa ya ƙara haifar da shakku kan makomarsa a siyasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Jigawa – Ana ta rade-radin cewa tsohon gwamnan Jigawa kuma tsohon ministan tsaro, Muhammed Badaru Abubakar, na iya rabuwa da APC bayan ya yi murabus.

Rahotanni sun bayyana cewa Badaru Abubakar zai iya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa ADC, duk da cewa ya fito ya karyata zancen.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Abba da ya yi murabus ya zama Shugaban APC bayan awanni a Kano

Rade-radin cewa gwamna Badaru Abubakar zai bar APC na kara karfi
Tsohon Ministan tsaron Najeriya, Badaru Abubakar Hoto: Abubakar Badaru
Source: Facebook

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa wannan jita-jita ta ƙara ƙarfi ne bayan wasu ayyuka da magoya bayansa suka yi a jihar Jigawa, musamman a shafukan sada zumunta.

Mutanen Badaru su na tare da Tinubu?

Wani daga cikin na kusa da shi, Zakari Kafin-Hausa, ya sake wallafa wani bidiyo inda wani malami daga Katsina ya soki manufofin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

A cikin bidiyon, Malamain ya yi zargin cewa shugaban na fifita yankin Kudu duk da goyon bayan da Arewa ta ba shi a zaben 2023.

Sai dai wasu ganawa da Badaru ya yi kwanan nan da manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa sun sa mutane da dama suna tambayar manufarsa.

Badaru ya gana da Sule Lamido da 'dansa
Tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido Hoto: Sule Lamido
Source: Facebook

A cikin mako guda, ya gana sau biyu da Mustapha Lamido, wanda shi ne dan takarar gwamnan jihar Jigawa na jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Haka kuma ya tattauna da wani tsohon Sanata kuma jigo a jam’iyyar ADC a jihar, Ubale Shitu.

Kara karanta wannan

APC ko ADC: Gwamna ya gaji da rikicin PDP, ya fara shirin sauya sheka don zaben 2027

Badaru na gana wa da yan adawa

Mafi daukar hankali shi ne ganawarsa da tsohon gwamnan jihar Sule Lamido, duk da cewa a baya akwai takaddama mai tsanani a tsakaninsu tun shekarar 2017.

A lokacin da Badaru yake gwamna, an gurfanar da Sule Lamido a kotu kan zarge-zarge guda hudu da suka hada da bata suna, tsoratarwa da kuma tayar da hankalin jama’a.

An tsare shi na wasu kwanaki a gidan yari na Kiyawa kafin daga baya kotu ta wanke shi daga dukkannin tuhume-tuhumen.

Saboda haka, sababbin ganawar da Badaru ke yi da wadannan ‘yan siyasa sun tayar da muhawara a fadin jihar.

Duk da haka, har yanzu yana cikin APC kuma yana da kyakkyawar alaka da gwamnan jihar Umar Namadi.

Tsohon minista ya yi magana bayan murabus

A wani labarin, kun ji cewa tsohon Ministan Tsaro a Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya yi karin haske game da yada jita-jita bayan ya yi murabus.

Kara karanta wannan

EFCC ta fito da Abubakar Malami, ta mayar da shi da iyalansa gaban kotu

Badaru wanda shi ne tsohon gwamnan Jigawa ya karyata rahoton da ya kira na bogi da ya ce ya yi murabus ne saboda adawa da harin Amurka da gwamnatin Bola Tinubu kan yan bindiga.

Ya bayyana labarin a matsayin sharri da ƙoƙarin bata masa suna tare da haddasa sabani tsakaninsa da Shugaba Tinubu da gwamnatin tarayya duk da ya bar kujerar minista.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng